Home Back

Abin Da Ya Fi Faranta Min Rai, Na Fi Karfin Ci Da Sha Ta Dalilin Sana’ata – Fateemah

leadership.ng 2024/8/24
Fateemah

Sana’a dai aba ce da ake samun rufin asiri a kowane yanayi na rayuwa, ta yadda mutum zai iya taimaka wa kansa ya taimaka wa waninsa. FATEEMAH MUHAMMAD, matashiya ce da ta rungumi harkar kasuwanci, wacce ta samu rufin asiri a cikinta duk da karatun Boko da ta yi amma hakan bai sa ta dogara da aikin albashi kadai ba. A wannan tattaunawar da suka yi da wakiliyarmu BILKSU TIJJANI KASSIM, ta ja hankalin mata kan yin sana’a domin irin alfanun da ta gani, inda ta ce sana’a na ba da ga mutum ya taimaka wa iyayensa har ma da karatu idan ya so, kamar yadda ta kasance a wannan tattaunawa.

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Suna na Fateemah Muhammad Sanee ni cikakkiyar ‘yar garin Hadejia ce a Jihar Jigawa na yi karatu a Garin Hadejia

Matar aure ce?
A’a ni ba matar aure ba ce budurwa ce

‘Yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?
Ni ‘yar kasuwa ce

Wanne iri kasuwanci kike yi?
Eh ina saida abubuwa daban-daban.

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?
Gaskiya ni ma’abociyar rataya jaka ce sannan kuma ina son sa abin hannu suna ba ni sha’awa sosai, kuma abin yana ba ni sha’awa idan na ga ‘yan uwana suna kasuwanci suna taimaka wa iyayensu sosai shi ne ya ja hankalina.

Mene ne matakin karatunki?
Yanzu ina aji na biyu a jami’a

Wanne iri kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
Eh to, kowacce sana’ar akwai kalubale a cikinta gaskiya kalubale na shi ne masu amsar bashi su ki biyanka da wuri shi ne kalubalena

Zuwa yanzu wannne iri nasarori kika samu?
Gaskiya na cimma nasarori da dama na taimaki kaina da iyayena Alhamdulillah da yan’uwana da kuma karatu na wannan ma babbar nasara ce a rayuwata

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Alhamdulillah abin da ya fi faranta min rai shi ne na ga na fi karfin ci da sha kuma ta dalilin sana’ata na fi karfinsu

Wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Ta intanet

Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?
Jajir cewa da juriya akan sana’ata

Wacce iri addu’a ne idan aka yi miki kike jin dadi?
Idan aka ce Allah ya jikan iyaye na to ina jin dadi wannan addu’ar sosai.

Wanne iri goyo baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Gaskiya ina samun goyan baya sosai akan karatu da kasuwanci.

Kawaye fa?
Eh toh, ba za’a rasa kawaye ba

Me kika fi so a cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Kayan sawa na fi son atamfa kayan kwalliya kuma kwalli

A karshe wacce iri shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Mata a yi karatu kuma a tashi a kama sana’a domai sana’a tana taimakawa wajen karatu da iyaye sosai.

People are also reading