Home Back

Noman Gwanda Da Kasuwancinta A Saukake

leadership.ng 2024/5/1
Noman Gwanda Da Kasuwancinta A Saukake

Ana samun dimbin kudin shiga a noman Gwanda a Nijeriya, amma babban abin taikaici shi ne, da yawan mutane ba su damu da yin nomanta ba.

Wasu masana a fannin, sun danganta rashin rugumar wannan fanni a kan rashin wayar musu da kai dangane da amfanin da ke tattare da noman na Gwanda.

Yadda Ake Renon Irin Gwanda:

Mataki na farko a noman Gwanda shi ne,  fara renon Irin da za a shuka na Gwandar.

Ka Tabbata Ka Sayo Ingantaccen Irin Da Za Ka Shuka:

Ka samu wajen da ya fi dacewa ka gyara tare da kone sharar da ke wajen, sai ka shuka Irin mita biyar tsakanin kowanne Iri haka, yana kai wa kimanin satuttuka kafin ya fara nuna ko kuma fiye da haka.

Bayan watanni biyu da shukawa, sai a nome ciyawar da ke gurin; sannan ka da kuma a zubar da ciyawar a bar ta a nan ta rube yadda za ta zama takin gargajiya.

Bayan wata daya zuwa biyu, sai a  canza mata waje; inda ake ganin zai fi gibin sama da mita biyar, bayan wata uku sai a sayo maganin feshi a yi wa kasar, wanda hakan zai sanya ta yin saurin girma.

Har ila yau, bayan wata shida sai a kara yin wani feshin, inda a cikin sati uku masu zuwa kacal za ta kara yin kyau, sai a bar ta zuwa wata uku ko fiye da haka, domin ta kara yin karfi.

Kasar Noman Da Ta Fi Dacewa:

Ka tabbatar da ka yi shuka a kasar noman da ta fi dacewa,  musammn don ka samu amfanin mai yawa,  haka nan ana so a yi shuka a kasar noman da ke da lema sosai.

Matakan Shuka Gwanda:

A wannan matakin, ana bukatar a ciro ta daga wadanda suka fara fitowa daga cikin abin da aka shuka Irin tun farko, sai a haka rami a shuka ta.

Lokacin  Da  Ya Fi Dacewa A  Shuka Ta:

Babu takamaiman lokacin da aka kebe na shuka ta, donin a kowane lokaci na kakar noma; za iya yin nomanta, har ila yau kuma ta na jure wa kowane irin yanayi.

Kwana Nawa Take Yi Kafin Ta Fara ‘Ya’ya?

Ya danganta da ingantaccen Irin da aka shuka da kuma yadda nau’in Gwandar yake, wasu na kai wa tsawon shekara hudu kafin su girma; tun daga lokcin da aka shuka Irin, haka nan kuma wasu na kai wa tsawon shekara takwas kafin su girma.

Lokacin Girbin Gwanda:

Yayin da jikinta ya fara canzawa zuwa yalo, sai dai wasu nau’in Gwandar, ba ya canzawa zuwa yalo idan sun nuna suna kuma kai wa wata tara bayan an canza wa Irin matsuguni daga inda aka dasa shi.

Bishiya daya ta Gwanda, za a iya samar da kimanin Gwanda daga 75 zuwa 100 a shekara, sannan ta na iya kaiwa tsawon shekaru dari ana cire ‘ya’yanta, amma an fi fara samun amfaninta daga shekaru uku zuwa hudu.

Kasuwancin Gwanda:

A yayin da ake jira ta kammala girma, sai a fara tuntubar masu bukatar saye ko kuma kasuwar da za a kai don sayarwa, haka nan za a iya tuntubar kamfanoni, musamman wadanda ke sarrafa ta zuwa wasu nau’ukan kayan lemon Kwalba, sarrafa magunguna da sauran makamantansu.

People are also reading