Home Back

Sojoji sun kashe Ƴan ta’adda 715, sun ceto mutum 465 a cikin kwanaki 30

premiumtimesng.com 2024/5/18
Ana batakashi tsakanin ‘yan ta’adda da Sojojin Najeriya a Madallah Abuja

Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa soji sun kashe ‘yan ta’adda 715, sun ceto mutum 465 a cikin kwanaki 30 da suka wuce.

Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.

Buba ya ce dakarun sun kama ‘yan ta’adda 1,146 a cikin wannan wata.

Ya ce sojojin sama da kasa sun kuma kai wa maboyar ‘yan bindiga kamar su Nasanda, Babaru, Kamilu Buzaru, Ali Dawud, Bakura Fallujah da Mallam Ari dake yankin Arewa maso Yamma hari inda suka ragargaza wuraren.

Sauran maboyar maharan da sojojin suka yi wa ruwan bama-bamai sun hada da Mallam Yadee dake karamar hukumar Mariga a jihar Neja da maboyar Bello Turji dake dajin Kagara dake tsakanin Shinkafa a jihar Zamfara da karamar hukumar Isa jihar Sokoto.

Buba ya ce nan ba da dadewa ba dakarun za su kama sauran maharan dake ganin suna cin Karen su babu babbaka a faɗin kasar nan.

Ya ce sojojin sun kwato bindigogi sama 937, harsasai sama da 23,034 da dai sauran su.

People are also reading