Home Back

SABON TSARIN BIN DIDDIGI: Tinubu zai farfaɗo da Majalisar Tantance Kwangiloli, wadda ta daina aiki tsawon shekaru 17

premiumtimesng.com 2024/8/22
Tinubu ya rattaba hannu kan sabon kudirin ba da lamuni na dalibai

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aika wa Majalisar Tarayya ƙudiri, wanda ya nemi amincewar sake farfaɗo da Majalisar Tantance Kwangiloli (National Procurement Council).

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, a ranar Laraba.

Idris ya ce, “maƙasudin yin hakan shi ne domin mu tabbatar da Majalisar Tantance Kwangiloli mai tasiri da karsashi ta kafu, wadda za ta riƙa duba da nazarin kowace kwangila ta gwamnatin tarayya, domin tabbatar da sahihancin adadin kuɗaɗen da za a kashe, mata, bisa tsarin dokokin gudanar da ayyukan kwangiloli.”

Haka kuma shi ma Ministan Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya ce Shugaba Tinubu ya yi magana dangane da tabbatar da samun daidaito tsakanin Dokar Kasafin Kuɗaɗe da kuma Dokar Bayar da Kwangiloli da kuma Dokar Bin-diddigin Kashe Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya.

“Tuni har ma Majalisar Zartaswa ta kafa kwamitin da zai sake duba Dokar Kwangiloli ta Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin Antoni Janar na Tarayya, kuma Ministan Shari’a.

“Shugaban ƙasa ya umarci dukkan ma’aikatun gwamnatin tarayya, hukumomi da cibiyoyin gwamnati su sake nazarin ayyukan kwangilolin da suka bijiro da su, ta hanyar bin ƙa’idar da ke tattare a cikin tsarin kasafin kuɗaɗe.

People are also reading