Home Back

HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA A KATSINA: Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta tabbatar da harin Gidan Kare a yankin Faskari

premiumtimesng.com 2024/6/29
Rundunar ƴan sandan Kano ta tsinci gawar wasu ma’aurata biyu kulle a ɗaki a Dawakin Tofa

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da kai harin da ‘yan bindiga suka yi a ƙauyen Gidan Kare, ranar Asabar cikin Ƙaramar Hukumar Faskari.

A ranar Lahadi PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka yi mummunan kisa a garuruwan Unguwar Lamiɗo da Gidan Kare, inda suka kashe mutum 23 a Gidan Kare, 14 kuma a Unguwar Lamiɗo.

Yayin da Unguwar Lamiɗo ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bakori, Gidan Kare kuma ya na ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Faskari.

Sai dai kuma bayan buga labarin, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta fitar da sanarwar a ranar Lahadi ɗin cewa a Unguwar Lamiɗo ne aka kai hari, amma ba ta yi maganar kisan da aka yi a Gidan Kare ba.

Kilomita biyu ne tsakanin Gidan Kare da Unguwar Lamiɗo, kuma maharan da suka shiga Gidan Kare, su ne dai suka kutsa Unguwar Lamiɗo.

Bayan fitar sanarwar ‘yan sanda, inda ta nemi ƙarin haske daga duk wanda zai iya bayar da wasu bayanai, wakilin mu ya tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Katsina, ASP Abubakar Saddiq-Aliyu. Ya bayyana wa wakilin su cewa, tabbas sun samu labarin harin da aka kai Gidan Kare, amma kuma su na kan bincike a daidai lokacin da wakilin na mu ya kira shi.

Binciken da PREMIUM TIMES ta ƙara yi, ta samu tabbaci daga majiya a cikin Gidan Kare, wanda ya nemi a sakaya sunan sa cewa tabbas mutum 23 aka kashe, kuma da shi aka yi aikin binne gawarwakin su da yi masu jana’iza.

“Waɗanda aka kashe ɗin a cikin gari aka kashe su. An kashe Ɗan Usumanu, wanda ake kira Lauje. Shi wannan yaron jami’in Dakarun Tsaro ne waɗanda Gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa kwanan baya.

“Sannan an kashe Sabi’u, wanda ake kira ‘Well Playa’, an kashe Sabi’u Gidan Zaki sai Shafi’u, Ɗan Ammani, Yakubu Hantsi, Yahaya Maifulani, Sagiru Garba da Hashim Lawal.”

Majiyar PREMIUM TIMES Hausa ta ce “akwai kuma Abubakar Maitsimi, mutumin Kuka Uku, shi ma ya zo tallar tsimi ƙauyen mu aka ritsa da shi, aka harbe shi. Sai wani tsoho shi ma daga Kuka Uku, an harbe shi a Gidan Kare.

“Waɗannan su zan iya riƙe sunan su a yanzu, saboda a waya na ke magana da kai.

“Da ni aka rufe su, an yi wa mutum 16 kabari ɗaya, wasu 5 kuma su ma na su kabarin ɗaya daban. Sai mata biyu da aka kawo daga baya daga asibiti, su kuma aka rufe su daban.” Inji majiyar da ta nemi a sakaya sunan ta.”

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum 31 suka kwashe shanu ƙarƙaf a yankin Bakori da Faskari.

A labarin ta ce dandazon ‘yan bindigar da aka haƙƙaƙe cewa sun kai 100, sun kashe mutum 31 a Gidan Kare da Unguwar Lamiɗo, kusa da Kakumi a Jihar Katsina.

Yayin da majiya ta bayyana wa wakilin mu cewa an kashe mutum 17 a Gidan Kare, ya ce mutum 14 aka kashe a Unguwar Lamiɗo.

Wannan mummunan kisa ya faru ne wajen ƙarfe 6 na yamma, a ranar Juma’a.

Majiyar PREMIUM TIMES Hausa ta tabbatar da cewa maharan waɗanda suka dira a kan babura, sun kai 100, kamar yadda wani jami’in tsaro ya tabbatar masa.

Ya ce shi dai bai ga maharan ba, dai gawarwaki kam sun kai 31.

Haka nan ya ce bayan maharan sun gama aika-aikar su a Gidan Kare, sun tattara shanun garin sun yi awon gaba da su, su ka bar gawarwaki 17 kwance a garin.

“Daga Gidan Kare sai suka wuce Unguwar Lamiɗo, tunda dama kusa-da-kusa ne. Sun kashe mutum 13 sannan suka tattara shanun garin, su ka haɗa da na Gidan Kare suka nausa daji da su.”

Yayin da Gidan Kare ke cikin Ƙaramar Hukumar Faskari, Unguwar Lamiɗo na ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bakori. Dukkan garuruwan su na kusa da Kakumi, kan hatsabibiyar hanyar zuwa Sheme daga Ƙanƙara, hanyar da aka taɓa yin garkuwa da Alaramma Ahmad Suleiman.

Wani ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES Hausa ta wayar tarho cewa a yanzu da ake rubuta labarin, “ina tabbatar maka akwai gawarwaki 14 an tara su cikin wani ɗaki a Unguwar Lamiɗo. Amma Gidan Kare an kashe mutum 17.”

Majiyar mu wanda ba ya so a bayyana sunan sa, ya ce sojoji sun isa wurin da safiyar Lahadi.

Waɗanda Aka Sace Tun Cikin Azumi Su Na Hannun ‘Yan Bindiga:

Majiyar ta mu ya yi wa wakilin mu ƙarin haske dangane da mutane 27 da aka yi garkuwa da su a garin Kwai da ke kusa da Ruwan Godiya, kuma kusa da Unguwar Lamiɗo da Gidan Kare.

“Daga cikin mutum 27 da aka sace bayan Sallar Tarawi a ranar 10 ga watan azumi, mun biya Naira miliyan 8 an sako mutum 16. Amma har yanzu mutum 11 na hannun su, tun cikin azumi, sun ce sai an cika masu Naira miliyan 2 sannan za su sako su, domin Naira miliyan 10 suka ce a biya su.” Cewar majiyar PREMIUM TIMES Hausa.

“Akwai surukai na biyu mata, ɗaya har da goyo a cikin su. Su ukun sai da aka biya Naira 400,000.00 kowace sannan aka sako su. Naira miliyan 1.2 aka biya, bayan an sayar da gonaki.”

Wata majiyar ta ce an yi jana’izar mamatan da safiyar yau Asabar.

People are also reading