Home Back

Manyan Malaman Addini Sun Gudanar da Addu'o'i Ga Tinubu, APC Ta Nemi Taimakon Allah

legit.ng 2024/7/3
  • Jam'iyyar APC a jihar Benue ta gudanar da addu'o'i na musamman ga Shugaba Bola Tinubu domin samun nasara a mulkinsa
  • Tawagar malaman addinin Kirista da dama ne suka jagoranci addu'o'in da aka gudanar a Makurdi da ke jihar Benue
  • Shugaban jam'iyyar a jihar, Austin Agada ya ce sun shirya addu'o'in ne ga Tinubu da kuma rashin tsaro da yajin aikin da ake yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Gamayyar malaman addinin Kirista da dama ne aka hada domin yin addu'o'i ga Shugaba Bola Tinubu.

Malaman sun kuma yiwa kasar Najeriya addu'ar samun nasara da yaye duka matsalolinta wanda jam'iyyar APC reshen jihar ta dauki nauyi.

An gudanar da addu'o'in ne a gidan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da ke birnin Makurdi a jihar a jiya Litinin 3 ga watan Yuni, cewar Punch.

Addu'o'in da aka gudanar a cikin coci da kuma fili ya samu halartar shugabannin jam'iyyar APC da kuma mambobinta da dama.

Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Austin Agada ya ce an gudanar da addu'o'in ne domin taya Shugaba Tinubu murnan cika shekara daya, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Agada ya ce an kuma yi addu'o'i domin neman taimakon Ubangiji wurin yaye matsalolin da ƙasar ke fama da su.

Ya ce sun roki ubangiji karin lafiya ga Tinubu domin samun kwarin guiwa da kuma matsalar yajin aiki da ake fama da shi na kungiyar kwadago.

"An shirya gudanar da addu'o'in ne domin Tinubu da Akume da kuma kasar Najeriya baki daya bayan cika shekara daya a kan mulki."
"An yi addu'o'in domin neman taimakon Ubangiji kan rashin tsaro da tattalin arziki da kuma wannan yajin aiki na NLC da ake yi."

- Austin Agada

Agada ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba Tinubu goyon baya a jihar dama yankin Arewa ta Tsakiya baki daya.

Kotu ya hana binciken Ortom a Benue

Kun ki cewa Babbar kotun jiha a Benue ta yi hukunci kan shirin binciken tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom.

Kotun ta haramtawa Gwamna Alia Hyacinth ci gaba da gudanar da bincike kan gwamnatin Ortom har sai an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

People are also reading