Home Back

EFCC ta Fara Binciken Sanata Rabi'u Kwankwaso kan Zambar Kudin 'Yan Fansho

legit.ng 2024/6/29
  • Rahotanni na bayyana cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta gayyaci tsohon gwamnan Kano kan zamba
  • An gayyaci sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin ya bayar da bayanai kan zargin da ake masa na almundahanar kudin 'yan fansho jagoran
  • Amma babban mai bawa gwamnan Kano shawara kan kafafen yada labarai Bashir Sanata ya shaidawa Legit cewa duk bita da kullin siyasa ce kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hukumar hana yiwa tattalin arzikin na kasa ta’annati (EFCC) ta mika goron gayyata ga jagoran APC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Hukumar ta bude binciken tsohon gwamnan na Kano da zambar kudin fansho da yawan su ya kai N2.5bn.

Rabiu Musa Kwankwaso
EFCC gayyaci Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan badakalar kudin 'yan fansho Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa tuni hukumar EFCC ta gayyaci Rabi’u Musa Kwankwaso, tare da yi masa tambayoyi kan zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya bawa EFCC bayanai

Wata majiya a hukumar ta EFCC ta bayyana cewa Sanata Kwankwaso ya yi tattaunawar keke-da-keke da masu bincike a hukumar.

Majiyar ta kuma kara da cewa tsohon gwamna a Kano, Kwankwaso ya bayar da muhimman bayan ikan zargin da ake masa na sama da fadi da kudaden ‘yan fansho.

Wata majiyar ta bayyana cewa za su ci gaba da binciken Rabi’u Musa Kwankwaso kan batun, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

‘Bita da kulli ake yiwa Kwankwaso,’ NNPP

Babban mashawarcin gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen yada labarai, Bashir Sanata ya yi zargin ana binciken ne domin rage kimar Kwankwaso.

Babban mashawarcin gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafn yada labarai, Bashir Sanata ya yi zargin ana binciken ne domin rage kimar Kwankwaso.

Amma y ace ko kadan hakan ba zai rage kimarsa a idanun wadanda suka sans hi ba, ganin cewar bas hi da son zuciyar da zai kwashi dukiyar talakawa.

EFCC za ta fara binciken Kwankwaso

A baya mun kawo muku labarin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta dauko binciken tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso.

An fara binciken ne a lokacin da ake tsaka da dambarwar masarautar Kano da ake ganin jagoran NNPP na da hannu a ciki, lamarin da ya musanta.

Asali: Legit.ng

People are also reading