Home Back

Ta Leko Ta Koma: Tinubu Ya Tsige Adekanmbi Kwanaki 2 Bayan Nada Shi Shugaban HYPREP

legit.ng 2024/8/23
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana korar Olufemi Adekanmbi a matsayin shugaban gudanarwa na shirin HYPREP
  • Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da nada shi shugaban hukumar, ya maye gurbinsa da tsohon shugaban da aka tube
  • Kamar yadda aka gano, an yi bitar kwazon Farfesa ]Nenibarini Zabbey, lamarin da yasa aka ce ya dace yacigaba da shugabantar hukumar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire Olufemi Adekanmbi daga matsayin shugaban na shirin magance matsalar gurbacewar iska na HYPREP.

Wannan na zuwa ne bayan sa'o'i arba'in da takwas bayan yi masa nadin. A hukumance an nada Adekanmbi wannan matsayin shugaban HYPREP ne a ranar Asabar.

Tinubu ya warware nadin da ya yiwa Olufemi Adekanmbi
Tinubu ya tsige Olufemi Adekanmbi daga shugaban shirin HYPREP. Hoto: @adekanmbi_olufemi, @officialABAT Asali: Twitter

HYPREP: Tinubu ya dawo da Farfesa Zabbey

A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya sanar da cewa Tinubu ya mayar da Farfesa Nenibarini Zabbey a matsayin shugaban HYPREP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Ngelale ya ce, wannan hukuncin ya biyo bayan bitar kwazon Fafesa Zabbey da Shugaba Tinubu yayi inda aka gano ya cancanci ya cigaba da rike matsayin.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da mayar da Farfesa Nenibarini Zabbey bakin aiki a matsayin shugaban shirin magance gurbacewar muhalli na (HYPREP)."

Muhammadu Buhari ne ya fara nada Zabbey

Sake dawo da Farfesa Zabbey ya fara aiki ne a nan take, kamar yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi umarni.

Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara nada Farfesa Zabbey a matsayin shugaban hukumar a watan Mayun 2023 bayan wa'adin Giadom Dumbari ya kare.

Duba sanarwar wadda Daddy Olusegun, mai tallafawa Shugaba Tinubu ta fuskar kafofin sada zumunta ya wallafa a shafinsa na X.

Tinubu ya kirkiro sabuwar ma'aikata

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kirkiro sabuwar ma'aikata a matakin tarayya.

Ya kirkiro ma'aikatar kiwon dabbobi wacce ake sa ran za ta magance matsalar manoma da makiyaya da ta ki ci balle cinyewa a fadin Najeriya.

An tabbatar da kirkiro sabuwa ma'aikatar ne yayin wani taron kaddamar kwamitin aiwatar da gyara a fannin kiwon dabbobi wanda aka yi a fadar shugaban kasan.

Asali: Legit.ng

People are also reading