Home Back

Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Ganduje Ya Sake Rokon Ƴan Najeriya

legit.ng 2024/7/9
  • Yayin da ake tsaka da rikicin masarautun Kano, shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya roki ƴan Najeriya kan mulkin Bola Tinubu
  • Ganduje ya ce tun yanzu tsare-tsaren da Tinubu ke dauka sun fara haifar da ɗa mai ido a cikin shekara daya da ya yi kan mulki
  • Shugaban ya bayyana haka ne yayin kaddamar da littafin cika Tinubu kwanaki 365 a kan mulkin Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya ce Shugaba Bola Tinubu ya shirya kawo sauyi akasar.

Ganduje ya ce tsare-tsaren da Tinubu ke dauka a kasar sun fara haifar da ɗan mai ido tun ba a je ko ina ba.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin taron kaddamar da littafi game da kwanaki 365 na Tinubu a Najeriya a birnin Tarayya Abuja, cewar The Nation.

Ya bukaci ƴan Najeriya da su kara hakuri a mukin Tinubu domin samun abin da ake nema na ci gaba a kasar, Punch ta tattaro.

"Ina son rokon ƴan Najeriya da su kara hakuri musamman a bangaren rashin tsaro da kuma tattalin arziki."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina da tabbacin cewa duka wadannan matsaloli an bayyana su a cikin wannan littafi da aka ƙaddamar."

- Abdullahi Ganduje

Shugaban APC a Amurka, Farfesa Tai Balofin da abokin aikinsa, Farfesa Bolu Folayan ne suka rubuta littafin.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading