Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Ganduje Ya Sake Rokon Ƴan Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya ce Shugaba Bola Tinubu ya shirya kawo sauyi akasar.
Ganduje ya ce tsare-tsaren da Tinubu ke dauka a kasar sun fara haifar da ɗan mai ido tun ba a je ko ina ba.
Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin taron kaddamar da littafi game da kwanaki 365 na Tinubu a Najeriya a birnin Tarayya Abuja, cewar The Nation.
Ya bukaci ƴan Najeriya da su kara hakuri a mukin Tinubu domin samun abin da ake nema na ci gaba a kasar, Punch ta tattaro.
"Ina son rokon ƴan Najeriya da su kara hakuri musamman a bangaren rashin tsaro da kuma tattalin arziki."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina da tabbacin cewa duka wadannan matsaloli an bayyana su a cikin wannan littafi da aka ƙaddamar."
- Abdullahi Ganduje
Shugaban APC a Amurka, Farfesa Tai Balofin da abokin aikinsa, Farfesa Bolu Folayan ne suka rubuta littafin.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng