Home Back

Ƴan Majalisa na so Gwamnatin Tarayya ta daina tura kuɗi ga shugabannin ƙananan hukumomi na riƙon da gwamnoni ke naɗawa

premiumtimesng.com 2024/8/22
ƘARIN ALBASHI: Bayan Tinubu ya ɗora Naira 2,000 kan Naira 60,000, Gwamnoni sun ce 60,000 ɗin ma ba za su iya biya ba

Bayan nazari ya gano cewa akwai jihohi 20 yanzu haka daga cikin 36 inda shugabannin riƙo ne ke riƙe da ƙananan hukumomi, Majalisar Tarayya ta yi kira ga Hukumar Raba Kuɗaɗen Gwamantin Tarayya (RMAFC), cewa ta daina tura wa kowace ƙaramar hukuma wadda shuganninn riƙo ne ke riƙe da ita, idan ba zaɓaɓɓu ba ne.

Hakan ya biyo bayan wani uziri da Ademorin Kuye, ɗan APC daga Legas ya gabatar, kuma aka samu amincewar majalisa a ranar Talata.

Kuye ya ce daga cikin jihohi 36 na ƙasar nan, 16 ne kaɗai aka yi zaɓen ƙananan hukumomi, saura kuma duk shugabannin riƙo ne da gwamnoni suka naɗa, wato jihohi 20 kenan.

Ya ce hakan ya saɓa wa Sashe na 7 na Kundin Dokokin Najeriya na 1999.

Wannan kira dai ya zo daidai lokacin da Kotun Ƙoli ta bai wa ƙananan ƙananan hukumomi cin gashin kai, ta haramta kuɗaɗen su shiga hannun gwamnonin jihohi.

Kotun Ƙoli ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya 774 ‘yancin cin gashin kan su.

Yayin da ta ke karanto hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, Babban Mai Shari’a Emmanual Agim ya ce Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa haramun ne daga yau Alhamis gwamnoni su riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Mai Shari’a Agim ya ce an shafe shekaru sama da 20 kenan ana fama da gwamnonin jihohi su daina riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke ba su, amma gwamnonin sun ƙi dainawa.

Ya ce tuni ƙananan hukumomi sun daina samun kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa gwamnonin jihohi domin su ba su.

Yayin da ya ce daga yau ƙananan hukumomi ne za su riƙa kula da kuɗaɗen su tare da kashe su ta hanyar yin ayyuka kai-tsaye daga hannun su, Agum ya yi fatali da jayayyar da gwamnonin jihohin 36 suka yi, inda su ka ce Antoni Janar na Tarayya ba shi da ikon shigar da gwamnonin ƙara a Kotun Ƙoli.

Ya ce Antoni Janar na da ‘yancin shigar da ƙara a kotu.

“Daga yau kada Gwamnatin Tarayya ta ƙara tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen su ta hannun gwamnonin jihohi.

Daga yau Gwamnatin Tarayya ta riƙa tura wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye a asusun bankin ta, ba ta hannun gwamnonin jihohi ba.” Haka hukumcin na Kotun Ƙoli ya tabbatar.

Idan ba a manta ba, cikin watan Mayu ne Kotun Ƙoli ta nemi gwamnoni 36 su gabatar da bayanan dalilin da ba su so a ɓamɓare ƙananan hukumomi daga ƙarƙashin su.

A wancan lokacin, Kotun Ƙoli ta umarci gwamnonin Najeriya 36 kowa ya aika da bayanan kare kai daga ƙarar da Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi ya shigar, inda ya nemi kotun ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ‘yancin cin gashin kan su da mallakar da gwamnonin jihohi suka yi masu.

Alƙalan Kotun Ƙoli bakwai ne suka zartas da umarnin a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Lawal Garba.

Kotun ta ce su kai bayanan kare kan su a cikin kwanaki biyar.

A ranar Alhamis ɗin ce dai aka fara zaman shari’ar.

Wannan jarida ta buga labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 Kotun Ƙoli, ta na so a bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su.

Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnonin Najeriya 36, inda ta ke roƙon kotu ta tirsasa ƙwatar wa ƙananan hukumomin ƙasar nan 774 cin gashin kan su, wato a riƙa ba su kuɗaɗen su kai-tsaye, ba tare da an bai wa jihohi su ba su ba.

Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a na Tarayya ne ya shigar da ƙarar a Kotun Ƙoli, ya na neman kotun ta bai wa ƙananan hukumomin cin gashin kan su.

A cikin ƙara mai lamba SC/CV/343/2024, gwamnatin tarayya na so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi.

Haka kuma ta na so a riƙa tura wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye, ba ta hannun gwnonin jiha na.

Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi na kuma so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni naɗa shugabannin riƙon ƙananan hukumomi.

An dai shirya za a saurari ƙarar a ranar 30 ga Mayu.

An daɗe ana ƙorafin yadda gwamnonin jihohi ke sarrafa ƙananan hukumomi.

Ko kwanan nan tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce zaɓen shugabanni ba shi da bambanci da taron naɗa basaraken gargajiya.

People are also reading