Home Back

El Rufai Ya Karɓi Baƙuncin Kwankwaso Kwanaki Bayan Kai Wa Buhari Ziyara a Daura

legit.ng 2024/7/6
  • Jagoran jam'iyyar NNPP kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ban girma ga Nasir El-Rufai
  • Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne a gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna na Abuja domin su gaisa da juna
  • Wannan ziyarar dai ta jawo cece kuce a kafofin sada zumunta, inda har wasu ke alakanta hakan da shirin siyasa yayin da ake tunkarar 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa na Abuja.

El-Rufai ya karbi bakuncin jagoran jam'iyyar NNPP ne kwanaki kadan bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Daura.

Kwankwaso ya yi magana kan ziyarar da ya kai wa El-Rufai
El-Rufai da Kwankwaso sun saka labule a Abuja. Hoto: @KwankwasoRM Asali: Twitter

Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar 27 ga Yuni cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau na kai ziyarar ban girma ga tsohon abokin aiki na, H.E Nasir El-Rufai a gidansa na Abuja."

Kalli hotunan ziyarar a ƙasa:

Ziyarar Kwankwaso ga El-Rufai ta jawo magana

Jim kadan bayan kai wannan ziyarar, kafar soshiyal modiya ta dauki zafi, inda wasu ke alakanta ziyarar da wani shiri na siyasa.

Duk da cewa bai fito fili ya alakanta kalamansa ga ziyarar da Kwankwaso ya kai wa El-Rufai ba, amma tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmed ya ce:

"Da alama dai 2027 za ta riske mu nan kusa"

Kalli maganar a nan ƙasa:

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Ina fatan dai shugaban kasa na sane da abubuwan da ake shiryawa. Ba shakka, zai iya zama abin hari a 2027. Ka watsar da naka, wanda kake so na kokarin watsa ka."

El-Rufai, Kwankwaso: "Jagororin siyasar Arewa"

Ma'abota amfani da kafar X sun cika a shafin Sanata Kwankwaso bayan wallafa hotunan ziyarar da ya kai wa El-Rufai, da yawansu na cewa:

"Yan siyasa biyu mafi daraja a Arewa. Shiyyar mu na alfahari da ku.
"Ku ne kaɗai mafi nagartar 'yan siyasa da muke da su a Arewa.
"Ya zama wajibi Arewa ta jira na tsawon shekara takwas kafin sake karbar mulki. Ba lallai ne ace Tinubu za a zaba a 2027 ba, amma dole a bar Kudu ta karasa wa'adinta"

El-Rufai ya ziyarci shugaban jam'iyyar SDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya ziyarci shugaban jam'iyyar SDP, Alhaji Shehu Gabam a ofishin jam'iyyar da ke Abuja.

Wannan ziyarar da El-Rufai ya kai ofishin SDP ya jawo cece kuce sosai a soshiyal midiya, musamman ganin cewa tsohon gwamnan ya rasa kujerar minista a gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

People are also reading