Home Back

Jami'an Tsaro Sun Cafke Wata Mata Mai Safarar Makamai Ga 'Yan Ta'adda a Katsina

legit.ng 2024/7/2
  • Jami’an tsaro sun kama wata mata Aisha Abubakar da ake zargi a jihar Katsina a lokacin da take ɗauke da alburusai da aka tanada domin ƴan ta’adda
  • Tun da farko matar ta ƙi amsa cewa harsasan na ta ne amma daga baya bayan an tsaurara bincike ta amsa cewa ita ce take ɗauke da su
  • Ta amsa cewa ta ɗauko harsasan ne daga jihar Nasarawa domin kai wa ga wasu ƴan ta'adda a Yan Tumaki cikin ƙaramar hukumar Dan Musa a jihar Katsina

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wata mata mai suna Aisha Abubakar da ake zargi da yin safarar makamai ga ƴan ta'adda.

Jami'an tsaron a jihar Katsina sun cafke matar ne ɗauke da alburusai lokacin da take kan hanyar kai su ga ƴan ta'adda.

An cafke mai safarar makamai ga 'yan ta'adda a Katsina
Dubun mai safarar makamai ga 'yan ta'adda ta cika a Katsina Hoto: @ZagazolaMakama Asali: Twitter

An cafke mai safarar makamai ga ƴan ta'adda

An dai gano alburusan ne lokacin da ake duba kayan da fasinjoji suka ɗauko ne, inda nan take ta musanta cewa alburusan na ta ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zagazola Makama wani masani kan harkokin tsaro a Najeriya da tafkin Chadi, ya sanya labarin cafke matar a shafinsa na X.

Sai dai, bayan an tsaurara tambayoyi, ta amsa cewa ta ɗauko alburusan ne daga jihar Nasarawa domin kai wa ga wasu ƴan ta'adda a Yan Tumaki cikin ƙaramar hukumar Dan Musa a jihar Katsina.

Wane martani ƴan Najeriya suka yi?

Ƴan Najeriya sun yi martani a shafukansa na X kan wannan lamarin da ya faru.

@ibrahimauwal614 ya rubuta:

"Abin da ya riƙa faruwa kenan a Maiduguri. Mutanen da aka gano suna tare da Boko Haram, ba a taɓa zato za su iya ba inda suke harka da kowa."
"Allah ne kawai ya sanya muka cire tsoro muka ga bayansu. Allah ya kyauta mana amma akwai matsala"

@Saiyph ya rubuta:

"Wannan ba addu'a ba ce kuma ba fata ba ne amma bisa abin da na ke gani kuma na ke karantawa, ba na tunanin za a iya kawo ƙarshen ƴan bindiga a nan kusa. Allah ya ci gaba da tona musu asiri. Mugaye kawai."

@dmancomeslow1 ya rubuta:

"Abubuwa irin waɗannan za su ci gaba da faruwa saboda mutane sun cire tsammanin cewa gwamnati za ta iya samar musu da tsaro."

An cafke mai safarar makamai ga ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an rundunar ƴan sandan jihar Plateau sun kama wani matashi mai matsakaicin shekaru da ake zargin yana ƙoƙarin kai wa ƴan bindiga makamai a Jos.

Wanda ake zargin ya isa garin Jos daga jihar Zamfara da kuma an yi nasarar cafke shi a lokacin da yake ƙoƙarin safarar makaman ga ƴan bindiga.

Asali: Legit.ng

People are also reading