Home Back

Majalisar Kano ta rushe sabbin Masarautun Ganduje, Sarki Sanusi zai dawo sarautar Kano

premiumtimesng.com 2024/9/28
Majalisar Kano ta rushe sabbin Masarautun Ganduje, Sarki Sanusi zai dawo sarautar Kano

Wannan mataki dai na nufin sarakuna 5 da waɗannan masarautu duk sun rasa rawunnan sarautar su.

A zaman karatun doka na biyu da aka yi a yau, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta rushe masarautun da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙiro guda huɗu, waɗanda suka haɗa da Gaya, Bichi, Rano da Ƙaraye.

Mambobin Jam’iyyar APC a Majalisar Dokokin Kano sun fice daga Majalisar yayin da ake yunƙurin yi wa Dokar Masarautu gyara.

Rahoton PREMIUM TIMES na ranar Laraba ya bayyana cewa Majalisar Dokokin Kano za ta yi gyare-gyare kan dokar da ta ƙirƙiro Sarakunan Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya.

Shekaru huɗu da rabi kenan bayan cire Sarki Muhammadu Sanusi II daga Sarkin Kano, yanzu kuma Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara nazarin dokokin da suka daddatsa Masarautar Kano gida biyar, har aka samar da sarakunan biyar a jihar.

Bayan samar da masarautun ne kuma aka cire Sarki Muhammadu Sanusi II, lamarin da ke cike da sarƙaƙiyar siyasa a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa Majalisar Dokokin Kano za ta gyara dokar da ta kafa sabbin masarautu.

A rahoton na BBC, “Majalisar dokokin Jihar Kano ta gabatar da batun yin gyara ga dokar da ta raba Masarautar Kano zuwa gida biyar wadda aka aiwatar a shekara ta 2019.

“Majalisar ta ɗauko batun gyaran dokar ne bayan Shugaban Masu Rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar da ƙudurin a Zauren Majalisa, a ranar Talata.”

A tattaunawar sa da BBC, Shugaban Masu Rinjaye ya ce : “Mun buƙaci a kawo dokar gaban Majalisa, domin yi mata gyare-gyare”.

Ya ƙara da cewa “gobe ko jibi za mu yi karatu na biyu na wannan doka a zauren majalisa.”

“Wannan na daga cikin alƙawari da jagoran mu ya faɗa”.

“Dama dai waɗansu ƙungiyoyi sun yi kira ga majalisar da ta duba dokar, tun bayan da jam’iyyar NNPP ta karɓi mulkin jihar a babban zaɓen Najeriya na 2023.

“A shekara ta 2019 lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje, Majalisar Dokokin jihar ta yi wa dokar Masarautar Kano garambawul, inda ta bayar da damar rarraba masarautar Kano zuwa gida biyar.

“A lokacin ne aka samar da sabbin masarutu huɗu, wato Rano da Karaye da Gaya da Bichi, tare da naɗa sarki mai daraja da ɗaya a kowace masarauta.

A yanzu Majalisa ta ce za ta sake dawo da dokar tare da yi mata gyaran fuska bayan zargin cewa an yi ta ne “ba bisa ƙa’ida ba kuma ba da kyakkyawar niyya ba.”

Ganduje ya sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II 9 Maris 2020.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya an ruwaito jagoran jam’iyyar NNPP mai mulkin Jihar ta Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na cewa akwai yiwuwar sake duba dokar ta da ta kafa sabbin masarautun na Kano.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a jihar ta Kano, Rabiu Kwankwaso wanda ake wa kallon shi ne uba a gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya ce an kafa masarautun ne da wata niyya ta daban wadda ba ta dace ba.

An tambayi Kwankwaso ko mai zai iya cewa game da lamarin masarautun jihar Kano, sai ya ce “Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma nasan dole za a zo a yi magana.”

“A duba a ga abin da ya kamata a yi a kai, gyara za a yi ko rusau za a yi,” in ji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya ce “ai gyara za a yi a kai” a don haka dole za a yi nazari kan dokar.

Tanadin Dokar Masarautun Kano Da Za A Yi Wa Gyare-gyare:

Dokar ta yi tanadi 51, kamar yadda Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana a lokacin da ta yi wa dokar gyara a shekara ta 2019. Haka dai BBC Hausa ta ruwaito.

People are also reading