An Samu Tashin Mummunar Gobara a Babbar Kasuwar Jihar Adamawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - An samu tashin mummunar gobara a kasuwar garin Yola da sanyin safiyar ranar Litinin.
Gobarar wacce ta tashi a kasuwar da ke ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ta lalata shaguna masu yawa, cewar rahoton jaridar Leadership.
Mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta ziyarci kasuwar da gobarar ta auku da safiyar ranar Litinin, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farauta ta bayyana cewa har yanzu ba a tantance girman ɓarnar da gobarar ta yi ba, inda ta yi alƙawarin ba ƴan kasuwar da abin ya shafa tallafi.
Farauta ta ce duk da ba a tantance adadin ƴan kasuwar da lamarin ya shafa ba, gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin rage musu raɗaɗi.
A kalamanta:
"Mun zo nan ne domin yi wa ƴan uwanmu maza da mata jaje waɗanda wannan gobarar ta shafa."
“Gwamnati za ta duba musabbabin abin da ya haifar da gobarar yayin da har yanzu ba a tantance adadin shagunan da suka ƙone ba."
Ta buƙaci ƴan kasuwar da su ɗauki ƙaddara kan gobarar tun da ba a rasa ran ko mutum ɗaya.
Shugaban ƴan kasuwar, Umar Abubakar, ya buƙaci gwamnati ta kawo musu ɗauki, inda ya bayyana cewa gobarar ta jawo ƴan kasuwa da dama sun rasa wuraren neman abincinsu.
Shugaban ƴan kasuwar, Umar Abubakar, ya buƙaci gwamnati ta kawo musu ɗauki, inda ya bayyana cewa gobarar ta jawo ƴan kasuwa da dama sun rasa wuraren neman abincinsu.
A wani labarin kuma, kun ji cewa an tafka asara bayan mummunar gobara ta tashi a kasuwar Balogun da ke Legas.
Gobarar wacce ta tashi a ɓangaren sayar da kayan kwalliya ta jawo asarar kayayyaki na biliyoyin Naira.
Asali: Legit.ng