Home Back

Za a iya fuskantar ruwan sama mai yawa da zai haddasa ambaliya a wasu jihohin Najeriya - NEMA

bbc.com 2024/7/1
Ambaliyar ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta yi gargadi a game da yiwuwar aukuwar gagarumin ruwan sama a garuruwa da dama na jihohin kasar, gami da Abuja babban birnin tarayya.

Al'amarin da hukumar ta ce ka iya haddasa ambaliyar ruwa a cikin mako mai zuwa.

Hukumar ta NEMA dai ta yi bayani cewa baya ga shirye-shirye irin na kandagarki da ake yi, ana kuma bin matakan fadakar da jama'a game da wannan matsala.

Mista Eugene Nyelong, babban jami'i ne a hukumar ta NEMA a shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya, ya shaida wa BBC cewa akwai wani rahoto da hukumar kula da yanayi ta Najeriya wato Nimet, ta fitar kan batun ambaliyar ruwan da ta yi hasashen zai afku a wasu bangarori na Najeriya a 2024.

Ya ce, bayan samun rahoton Nimet, hukumarsu ta NEMA, ta rubuta wasiku inda ta aikewa jihohin Najeriyar da ake hasashen za su fuskanci ambaliyar ruwa domin ankarar da su a kan hasashen Nimet.

“Mun sanar da jihohin don su fara daukar matakan kariya daga ambaliyar ruwan da aka yi hasashe, kuma tuni hukumarmu ta fara zagawa zuwa jihohi don wayar wa mutane kai a kan illolin ambaliyar ruwa da kuma matakan da ya kamata a dauka don kare afkuwar ambaliyar.”

Mista Eugene Nyelong, ya ce a cikin rahoton an zayyano jihohi 31 da ake ganin akwai yiwuwar su fuskanci ambaliyar ruwa, da kuma kananan hukumomi 144 da suma ake ganin ambaliyar za ta iya shafa.

Babban jami’in NEMA, ya ce “ Batun sauyin yanayi da toshewar magudanan ruwa da kuma gine-ginen da ake a kan hanya na daga cikin dalilan da ke haddasa ambaliyar ruwa.”

Ya ce, shi ya sa suka fara wayar da kan jama’a a kan yashe magudanan ruwa da kuma daina gini a kan hanya inda suke bi gida-gida da masallatai da makarantu da kasuwanni har ma da majami’u.

Yayin da damunar bana ta fara kankama, tuni hukumomi a wasu jihohin arewacin Najeriya suka fara daukar matakai domin gujewa illolin ambaliyar ruwa a yankunansu.

Jihohi kamar Jigawa da Yobe da Neja da dai sauran su, tuni suka fara gyaran magudanan ruwa da muhallai domin kaucewa afkuwar bala'in ambaliya ruwan a bana.

Jihohin sun yi la’akari ne da irin dumbin asarar da ake tabkawa da ta shafi rayuka da dukiyoyi sakamakon ambaliyar ruwa shi ya sa gwamnoni wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriyar suka dauki irin wadannan matakai.

Ana yawan samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya a kowacce shekara, abin da ya sa hukumar NEMA, ke yawan gargadin jihohi da ma mutane a kan daukar matakan kariya daga ambaliyar.

People are also reading