Home Back

KISAN SOJOJIN NAJERIYA: Gwamnatin Abiya za ta biya ladar Naira miliyan 25 ga wanda ya yi sanadin kama makasan sojoji huɗu a Aba

premiumtimesng.com 2024/6/26
ABUJA TA DAGULE: Bayan garkuwa da mutum 11 a Dutse-Alhaji, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum 23 a Bwari

Gwamnatin Jihar Abiya ta bayyana cewa za ta biya ladar Naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanan da aka bi har aka kama waɗanda suka kashe Sojojin Najeriya huɗu a garin Aba, babban birnin jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Okey Kanu ne ya bayar da wannan albishir a ranar Juma’a.

Ya nuna takaicin yadda wasu tsiraru ke neman maida ci gaban da aka samu a jihar baya.

Ya ce duk wanda ya bayar da bayanin da aka bi har aka kama waɗanda suka yi kisan na ranar Alhamis, to za a ba shi ladar Naira miliyan 25, kuma komai a sirrance za a yi, ba za a fallasa shi ba.

A na su ɓangaren, ‘Sojojin Najeriya za su yi wa IPOB luguden ramuwar-gayya’, kamar yadda Hedikwatar Tsaro ta tabbatar.

Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ɗauki alwashin yin ramuwar-gayyar kisan sojojin Najeriya 4 da ‘yan bindigar IPOB suka yi a Aba, babban birnin Jihar Abiya, a Kudu maso Gabas.

Waɗanda suka kashe sojojin dai suka tirsasa zaman gida tilas ne da tsagerun IPOB suka ƙaƙaba a yankin jihohin da ƙabilar Ibo suke, domin tunawa da zagayowar Ranar Biafra, wadda ake yi duk shekara a yankin.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Edward Buba, ya bayyana a ranar Juma’a cewa Sojojin Najeriya za su ɗauki fansa kan mambobin IPOB waɗanda suka kashe sojoji 4.

“Tabbas akwai muhimmancin mu ɗauki fansar wannan ta’addanci kan sojojin mu. Sojoji za su yi masu luguden ramuwar gayya.

“Za mu nuna masu ƙarfin sojoji sosai, za mu mamaye su domin mu ruguza gungun su baki ɗaya,” cewar Manjo Janar Buba.

Ranar Alhamis PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa ‘yan bindiga sun bindige Sojojin Najeriya 4 a garin Aba, sun banka wa motar su wuta.

Aƙalla Sojojin Najeriya huɗu aka kashe ranar Alhamis a garin Aba, babban birnin Jihar Abiya.

Aba ne gari mafi ƙarfin hada-hadar kasuwanci a yankin Kudu maso a Najeriya.

PREMIUM TIMES ta ji cewa ‘yan iskan gari kamar su 15 ne suka kai wa sojojin farmaki wajen ƙarfe 8 na safiyar yau Alhamis, a wani shingen binciken kan titi a Mahaɗar Titina dake Obikabia, cikin garin Aba.

An ce ‘yan bindigar su na tirsasa wa kowa ya zauna a gida tilas, kamar yadda ƙungiyar taratsin a-ware ta IPOB ta bada umarni a yankin na jihohin Kudu maso Gabas, domin tunawa da zagayowar ranar Biafra, wadda a kowace shekara ake murnar zagayowar ta a yankin.

Wanda aka yi kisan kan idon sa mai suna Marvelous ya shaida wa wakilin mu cewa maharan waɗanda suka rufe fuskokin su, sun dira wurin kuma nan take suka buɗe wa sojojin wuta.

Marvelous ya ce an kashe sojoji huɗu, wani soja ɗaya kuma ya ji mummunan rauni.

“An kashe soja huɗu. Ɗaya kuma an ji masa rauni da harbin bindigar da aka yi masa.” Inji Marvelous, Wanda yayi magana da wakilin mu da Turancin ‘pidgin’.

Maharan su na cikin baƙar Highlander (SUV). Har wasu farar hula su ma an ji masu raunuka yayin harbin.” Inji shi.

Dama an riƙa nuna wani bidiyo a soshiyal midiya, wanda ke ɗauke da waɗanda suka kai wa sojojin hari a cikin baƙar mota.

PREMIUM TIMES ta kalli bidiyon, kuma ta lissafa aƙalla mahara 10.

Har yanzu dai sojoji ba su ce komai ba tukunna.

People are also reading