Home Back

An Samu Raunuka Bayan Makiyaya Sun Farmaki Jami'an Tsaro

legit.ng 2024/10/5
  • Wasu makiyaya sun kai farmaki kan jami'an tsaro na rundunar tsaro ta Amotekun a jihar Ondo yayin da suke a bakin aiki
  • Makiyayan sun farmaki jami'an tsaron ne bayan sun kori shanunsu da ke yin ɓarna a wasu gonaki a jihar
  • Kakakin rundunar Amotekun na jihar, ya bayyana cewa makiyayan sun raunata wasu jami'an rundunar bayan sun farmake su da kwalabe, adduna da bindigu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Makiyaya sun raunata jami’an hukumar tsaro ta jihar Ondo (Amotekun) a ƙaramar hukumar Akure ta Arewa.

An kai harin ne yayin da jami’an Amotekun ke kokarin tabbatar da dokar hana kiwo a Igoba, a kusa da hanyar Ado.

Makiyaya sun farmaki jami'an Amotekun a Ondo
Makiyaya sun farmaki jami'an tsaron Amotekun a Ondo Hoto: @Naija_PR, @KadunaResident Asali: UGC

Yadda makiyaya suka farmaki jami'an Amotekun

Jami'an tsaron na korar shanu ne da ke yin kiwo a cikin wata gona lokacin da makiyayan suka farmake su da duwatsu, kwalabe, adduna da bindigu, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar Amotekun na jihar Ondo, Jimoh Adeniken, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya bayyana cewa wasu manoma ne suka kai jami'an zuwa gonakin inda suka tarar da sama da shanu 120 suna ɓarna a gonakin kuma babu makiyayi ko ɗaya a tare da su.

Jimoh Adeniken ya ce jami'an na Amotekun sun kora shanun daga cikin gonakin amma sai makiyayan suka kai musu farmaki.

"Makiyayan sun ci gaba da jefo duwatsu da kwalabe har sai da suka hau kan babbar hanyar tare da sumar da ɗaya daga cikin jami'an a wajen ƙoƙarin ƙwace makaman jami'an rundunar Amotekun."
"Sauran jami'an sun samu raunuka daban-daban a yayin harin inda ake duba lafiyarsu a asibiti."
"An gano mamallakin shanun yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike."

- Jimoh Adeniken

Rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutum biyu sun rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa.

Lamarin ya auku ne bayan wasu baƙin makiyaya da suka taho daga jihar Katsina sun sake kunna wutar rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙananan hukumomi uku na jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading