Home Back

Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano Naira Miliyan 10 Kan Tauye Hakkin Sarki Aminu Ado Bayero

leadership.ng 2024/7/3

Kotu ta bayar da umarnin Gwamnatin Kano ta bai wa Alh. Aminu Ado Bayero, tarar miliyan 10 na tauye masa hakki.

Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano Naira Miliyan 10 Kan Tauye Hakkin Sarki Aminu Ado Bayero

Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta bai wa Gwamnatin Kano Umarnin bai wa, Sarkin Kano 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, Naira miliyan 10,000,000 saboda tauye masa hakkin da tauye masa ‘yanci da walwala.

Kazalika kotun ta ce Sarkin na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, yana da damar yin yawo a ko ina a Nijeriya.

Kotun ta sake jaddada ikonta na sauraren shari’ar da Sarki Aminu Ado ya shigar gabanta.

Wannan hukuncin ya biyo bayan umarnin da Gwamnan Jihar Kano ta bayar na jami’an tsaro su kama shi ba tare da gamsasshen dalili ba.

A jiya Alhamis kotun ta zauna inda ta dage zaman zuwa yau gabanin yanke wannan hukuncin kan dambarwar Masarautar Kano tsakanin Sarkin Kano na 14/16 Malam Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

People are also reading