Home Back

Me rashin halartar Nijar da Mali da Burkina Faso taron Abuja ke nufi?

bbc.com 2024/5/5
Nijar Mali

Asalin hoton, Getty Images

Mahalarta babban taron Afirka kan yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a Abuja sun yi mamakin rashin ganin wasu ƙasashen yankin Sahel a wurin taron, bisa la'akari da irin muhimmancinsu a batun.

Ƙasashen da ba su halarci taron ba su ne jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso waɗanda tun a watannin baya suka yi shelar ficewa daga ƙungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma, Ecowas ko Cedeao.

A ƙarshen taron na Abuja wanda Najeriya ta shirya bisa haɗin gwiwar ofishin daƙile ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya, an ga buƙatar Afirka ta kafa rundunonin sojoji masu ƙarfi da ƙwarewa da kayan aiki, bisa aƙidar kishin Afirka da kishin ƙasa, ba tare da nuna ɓangaranci ba.

Taron ya ce nan gaba kaɗan za a sanar da rana da kuma wurin da za a yi wata ganawar, don bin sawun matakan da taron na Abuja ya cimma.

To yanzu abin tambaya shi ne ko za a iya cimma daƙile ta'addanci a Afirka ko kuma yankin Sahel ba tare da ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ba?

'Abin da kamar wuya'

Barista Bulama Bukarti wanda masanin tsaro ne kuma lauya mai zaman kansa a Burtaniya ya shaida wa BBC cewa "lallai rashin samun wakilcin Nijar da Mali da Burkina Faso ba ƙaramin giɓi ba ne a taro a ce an yi taro a Najeriya amma waɗannan ƙasashe ba su halarta."

Ya ci gaba da cewa " idan ka duba manya-manyan ƙalubalen tsaro da muke fuskanta guda uku, biyu daga cikinsu na faruwa ne a iyakar Najeriya da Nijar. Misali matsalar shigar da ƙwayoyi zuwa Najeriya ba zai yiwu ba idan ba a haɗ kai da Nijar ba. Haka kuma matsalar tsaro da arewa maso yammacin Najeriya da matsalar Boko Haram da arewa maso gabashin ke fuskanta duk sai an haɗa da Nijar." In ji Bukarti.

Barista Bukarti ya ƙara da cewa dole ne "a gudu tare a kuma tsira tare" kasancewar ƙasashen nan na manne da juna kuma duk abin da ya sami wata to fa "dole sai ɗayar ta kawo ɗauki za a iya magance.

Ai su kansu ƙungiyoyin ta'addancin haɗa kansu suke yi wajen ƙaddamar da hare-haren ta'addanci. To idan ƙungiyoyin za su haɗe kansu ina ga ƙasashen? Ka ga ai ƙungiyoyin sun ma fi su dabara. Dole ne su haɗu domin babu ƙasar da za ta iya cimma wani abu ba tare da wata ba." In ji barista Bukarti.

'Rundunar ko-ta-kwana za ta samu matsala'

Babban taron na Afirka kan yaƙi da ta’addanci dai ya yi kiran da a kafa rundunar Ko-ta-Kwana ta Afirka sannan su kama aiki gadan-gadan da nufin murƙushe ‘yan ta’addan da suka addabi sassan nahiyar.

To sai dai barista Bukarti ya ce wannan rundunar ba za ta yiwu ba idan dai har ƙasashen ba su haɗ kansu ba.

"Ya kamata ƙasashen nan su fahimci cewa batun tsaro ba na siyasa ba ne. Matsala ce da ta shafi kowa sannan ba ruwanta da ƙasar da ake mulkin dimokradiyya ko mulkin soja. Matsala ce wadda take iya cin kowa." In ji Bukarti.

Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso dai a lokuta da dama sun sha nesanta kansu daga yin ƙawance da wasu ƙasashen Afirka kamar Najeriya da ma yin shelar ficewa daga ƙungiyar Ecowas sakamakon sanya musu takunkumai tun bayan yin juyin mulki a ƙasashen.

People are also reading