Home Back

'Aiwatar da hukuncin kisa ya ƙaru a duniya'

bbc.com 2024/7/6
,
  • Marubuci,
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Mintuna 3 da suka wuce

Yawan aiwatar da hukuncin kisa ya ƙaru a duniya kamar yadda alƙaluman da hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam ta duniya ta Amnesty International ta fitar suka nuna.

Ƙungiyar ta samu alƙaluma 1,153 na kisan a 2023, ƙarin kashi 31 cikin ɗari daga kisa 883 da aka sani a 2022. Waɗannan su ne alƙaluma mafiya girma da ƙungiyar ta Amnesty International ta tattara tu 2015, lokacin da ake da kisa 1,634.

Babbar Sakatariyar ƙungiyar ta Amnesty Agnès Callamard ta bayyana cewa tashin gwauron zabi da aka samu na yawan aiwatar da hukuncin kisan yawanci ya kasance ne a Iran.

Ta ce hukumomin Iran suna nuna rashin mutunta rayuwar ɗan'Adam, inda suke aiwatar da hukuncin kisa hatta a kan laifukan da suke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi, tana mai arin bayani da cewa wannan na nuni da yadda hukumomin Iran ke nuna wariya ga al'ummar ƙasar mai rauni.

Duk da cewa rahoton ya nuna cewa Iran ta aiwatar da yawancin hukuncin kisan da aƙalla kisan mutum 853, Amnesty na gani China ce ta fi aiwatar da hukuncin kisa a duniya.

Duk da cewa babu wasu alƙaluma da China ta fitar na aiwatar da hukuncin kisa to amma Amnesty ƙiyasi ya nuna dubban mutane aka kashe a ƙasar a shekarar da ta wuce.

Amnesty ta kuma lura cewa hukuncin kisa da aka yanke a duniya ya ƙaru da kashi 20 cikin ɗari a 2023.

Wannan shi ne hukuncin kisa mafi yawa da aka yanke tun 2018.

Chart showing global executions and death sentences by year
Bayanan hoto, Teburin da ke nuna yawan masu laifi da aka zartar wa hukuncin kisa da kuma wadanda aka yanke wa hukuncin kisa

Waɗanne ƙasashe ne suka fi aiwatar da hukuncin kisa?

Amnesty ta ce ƙasashe biyar da suka fi aiwatar da hukuncin kisa a 2023 su ne, China, da Iran, da Saudiyya, da Somalia da kuma Amurka.

Iran kaɗai tana da kashi 74 cikin dari, yayin da Saudi Arabia take da kashi 15 cikin ɗari.

To amma a kan China, Amnesty, ta ce ba ta da alƙaluma da hukumomi suka fitar, kamar yadda ba ta da su daga Koriya ta Arewa da Vietnam, da Syria, da Falasdinu da kuma Afghanistan.

.
Bayanan hoto, ...

Ƙasashe nawa ne suka soke aiwatar da hukuncin kisa?

Yawan ƙasashen da suka soke hukuncin kisa ya ƙaru da daga 48 a1991 zuwa 112 a 2023.

Ƙasashe tara sun aiwatar da hukuncin a kan manyan laifuka, yayin da ƙasashe 23 da suke da dokar ba su aiwatar da hukuncin ba a cikin aƙalla shekara goma.

Ta yaya ƙasashen duniya ke aiwatar da hukuncin kisan?

Akwai hanyoyi huɗu da aka fi sani waɗanda ake bi wajen aiwatar da hukuncin a 2023, inda Saudiyya ce kaɗai ke fille kai.

Ƙasashe bakwai suna amfani da rataya, shida ta hanyar harbi, yayin da uku suka yi amfani da allurar guba a bara.

Babban jami'in majalisar Duniya mai kula da kare haƙƙin ɗan'Adam Volker Türkya ce, abu ne mai wuya a iya danganta aiwatar da hukuncin kisa da mutunta dan'Adam, da ƴancin rayuwa na mutum, da yin rayuwar da ba ta da azabtarwa ko gana aƙuba ko ƙasƙantarwa ko kuma hukunta mutum.

.
Bayanan hoto, Ƙasashen da ke yawan kashe masu laifi tsakanin 2019-2023

Wanke mutum

Wanke mutum, shi ne bayan an yanke masa hukuncin kisa, ya ɗaukaka kuma bai yi nasara ba, yayin da yake zaman jiran aiwatar da hukuncin, sai daga baya a wanke shi daga laifin a kuma sallame shi da cewa ba shi da laifi a hukumance.

Amnesty International ta samu irin wannan har guda tara a ƙasashe uku inda aka wanke fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa amma daga baya aka wanke su . Ƙasashen su ne : Kenya (mutum 5), Amurka (mutum 3), Zimbabwe (mutum1).

Masu rajin kare haƙƙindan'Adam na yaƙi da yanke wa mutane hukuncin kisa, domin nuna aibun yanayin da ake samu na wanke mutum bayan an riga an aiwatar da hukuncin wato an kashe mutum.

Hukuncin kisa domin zama darasi

Ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗikin Duniya ya ce, ƙasashe suna yin hukuncin kisa ne domin ya zama darasi- wato hana mutane aikata laifi.

Abin da yawancin masana kimiyyar halayyar dan'Adam suka yi amanna da shi shi ne cewa yarda da cewa hukuncin kisa na hana aikata laifi, babu sheda da ta tabbatar da haka a cewar masanan.

Wasu sun ce abin da ke hana yawanci aikata laifi shi ne yuwuwar kama mutum da kuma hukunta shi.

A shekara ta 1988 an gudanar da wani bincike ga Majalisar ɗinkin duniya domin gano alaƙar hukuncin kisa da yawan kisan kai. An kuma sabunta wannan a 1996. Daga nan ne aka zartar da cewa bincike ya kasa tabbatar da sheda ta kimiyya cewa hukuncin kisa ya fi tasiri a kan ɗaurin rai da rai.

Amurka
Bayanan hoto, Amurka na amfani da wani gado don zartar da hukuncin kisa bayan yanke hukuncin

Tasirin hukunci kisa a zukatan yara

A 2010, ƙasashe14, da suka haɗa da Algeria, da Argentina, da Kazakhstan, da Mexico da kuma Turkiyya, sun haɗu suka kafa wata hukuma da ke yaƙi da hukuncin kisa.

Hukumar ta ƙaru zuwa ƙasashe 24 da suka haɗa da Birtaniya da Kanada da Australia, da Jamus da Togo.

A cikin rahoton da ta fitar a baya-bayan nan, hukumar ta jaddada cewa, yara na fuskantar barazanar kisa a kasashe da dama, duk da yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya kan hakkin yara, ta haramta yin hakan. Yarjejeniyar na aiki a kasashe 196.

Ƙungiyar Ƙwararrun Masana halayyar ɗan'adam (APA) ta yi kira ga jihohin Amurka su haramta aiwatar da hukuncin kisa ga duk ɗan ƙasa da shekara 21.

APA ta rubuta cewa: “Bisa ga yanayin kimiyya da ake ciki a yanzu, ba za a iya cewa kwakwalwar ’yan shekara 18 zuwa 20 ta bambanta da na ’yan shekara 17 ba.”

Ta ci gaba da cewa: “Halayen ƙuruciyar matasa na tabbatar da rashin zartar da hukuncin kisa a kan yara masu shekaru 16 da 17 suna cikin ’yan shekara 18 zuwa 20.”

Yara ba kawai abin ya shafa ta hanyar kisa ba. "Ba kamar sauran nau'in hukunce-hukuncen laifuka ba, zartar da hukuncin kisa ga iyaye na daɗewa a zukatan yara," in ji Hukumar.

People are also reading