Home Back

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ƴar Takarar Gwamna da Wasu Shugabannin Jam'iyya 4

legit.ng 2024/7/2
  • Yayin da ake tunkarar zaben gwamna, APC ta dakatar da ƴar takarar da ta nemi tikitin gwamna a zaɓen fidda gwanin Ondo, Folake Omogoroye
  • Jam'iyya mai mulki ta kuma dakatar da wasu shugabannin APC a gudumar Ode Aye da ke ƙaramar hukumar Okitipupa a jihar Ondo
  • A sanarwan da jam'iyyar ta fitar, ta ce ta dakatar da ƴan takarar ne bisa zargin cin amana da yi wa APC zagon ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - All Progressives Congress (APC) ta gundumar Ode-Aye a karamar hukumar Okitipupa a jihar Ondo ta dakatar da Injiniya Folake Omogoroye.

Omogoroye, ita ce ƴan takara mace da ta fafata a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar ranar 20 ga watan Afrilu, 2024.

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.
Jam'iyyar APC ta dakatar da ƴan takarar gwamna mace a jihar Ondo Hoto: APC Nigeria Asali: Twitter

Ita ce ‘yar takarar gwamna ta baya-bayan nan da APC ta dakatar bayan irin wannan matakin ladabtarwa da aka dauka kan Sanatan Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta dakatar da ƴan takarar tare da wasu shugabannin jam'iyya huɗu na gundumar Ode Aye I, kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.

Waɗanda aka dakatar tare da Omogoroye sun haɗa da sakataren tsare-tsaren jam'iyya, Ayesan Tunde da mataimakin kakakin jam'iyya, Jemiken Seyi.

Sauran sune mataimakin sakataren walwala, Adebayo Omobayo da kuma mataimakin ma'ajiyin APC duk a gundumar, Eweje Omotayo.

Dakatar da Omogoroye na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na gundumar, Akinsowola Awodele. 

A cewar wasikar, an dakatar da Omogoroye ne saboda, "zargin cin amanar jam'iyya da kuma rashin biyayya ga shugabannin da aka naɗa."

Idan baku manta ba ƴar takarar gwamnan na cikin waɗanda suka yi fatali da sakamakon zaben fitar da gwanin wanda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya samu nasara.

Ta kuma yi kira da. soke zaɓen gaba ɗaya saboda an tafka kura-kurai kuma ta shigat da ƙara kotu inda ta ƙalubalanci nasarar Gwamna Aiyedatiwa.

APC na shirin kwace Kudu maso Gabas

A wani rahoton kuma mai neman takarar kujerar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar APC, Paul Chukwuma ya yi magana kan muradunsa na takara.

Paul Chukwuma ya ya sha alwashin cewa gaba daya jihohin Kudu maso Gabas za su dawo karkashin APC idan ya zama gwamna.

Asali: Legit.ng

People are also reading