Home Back

Matsalolin Gidan Aure (4) Mijina Ba Ya Kula ‘Ya`yana

leadership.ng 2024/6/29
aure

Assalamu alaikum masu karatu barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.

A yau shafin na mu zai ci gaba da kawo muku matsalolin gidan aure da yadda za a magance su: Abin da za mu tattauna a yau shi ne batun kula ‘ya`ya. Tabbas kowace uwa tana so ta ga yadda mijinta yake son ‘ya’yan da ta haifa masa. Ko ba ma shi da ya haife su ba, uwa takan ji dadi idan mutane suka so mata ‘ya’ya, shi ya sa ma aka ce “maso uwa ya so ‘ya’yanta”, to ina ga uban da kuma ya haifo su? Sai dai uwargida, yana da kyau ki sani, kafin ki zargi maigida rashin kula miki da ‘ya’ya ke ya kamata ki koya wa ‘ya’yanki yadda za su kula da babansu.

Da safe ki koya musu gaishe shi da zarar ya fita dama kamar jiran sa suke su je su gaishe shi, haka da yamma yana dawowa ki koya musu yadda za su tare shi idan mai mota ne da zarar sun ji shigowarsa su je su jira ya yi fakin su bude masa kofa, su yi masa sannu da zuwa, idan akwai kaya su debo.

Sannan ki koya musu sanin matsayinsa a wajensu da kuma yadda za su girmama shi fiye da kowane mutum a duniya, da yadda za su rika jin tsoran duk wani abin da zai bata masa rai, sannan kuma su so duk wani abin da zai faranta masa rai. Idan kika koya wa ‘ya’yanki haka za ki ga yadda babansu zai rika son su yana jan su a jikinsa.

Yaya tsaftarsu? Ya kamata ki kasance mai tsaftace ya’yanki a koda yaushe wanka wanki guga, matan kuma kitso akai-akai, maza aski idan gashi ya fito. Sannan ki hana ‘ya’yanki bata kayansu idan suna kanana, idan za su ci abinci ki cire musu kaya saboda kar ya baci, bayan sungama sai ki maida musu kaya.

Dawa yaran suke harka? Ya kamata ki zama mai sa ido akan ‘ya’yanki ki san dawa suke hulda, da wadanne irin abokai suke mu’amalarsu?.

People are also reading