Shugaba Cyril Ramaphosa ya sha rantsuwar kama aiki
Shugaban na Afirka ta Kudu kenan Ciryl Ramaphosa na shan rantsuwar kama aikin a gaban duban jama'a. Shugabannin kasashe kusan 20 na duniya, da suka hada da na Chaina da Masar da Cuba da Zimbabwe, da Najeriya,da Angola da Falasdinu suka halarci bikin. Jamiyyar ANC ta yi hadaka da jamiyyar Democratic Alliance DA, da kuma Inkata Zulu domin samun rinjaye don kafa gwamnati.