Home Back

Yadda ruwa ya yi awon gaba da tashar ruwa da ake kai wa Gaza tallafi

bbc.com 2024/6/18
..

Asalin hoton, Getty Images

Ruwa mai ƙarfi ya yi awon gaba da wata tashar wucin gadi da sojin Amurka suka gina domin kai tallafi cikin Gaza, wadda jami'an Amurka suka ce za a kwashe aƙalla mako guda kafin a gyara tashar.

Sojojin Amurka ne dai suka fara gina tashar ta kan ruwa wadda ke haɗe da ruwan Gaza, 'yan makonni da suka gabata.

Yanzu dai an rawaito cewar gadar da ake bi ta kai ga tashar ta wucin gadi ta ɓalle kuma dole sai an gyara ta kafin ta koma kamar yadda take domin ci gaba da kai kayan na agaji.

Ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗi cewar tallafin da ke shiga Gaza bai taka kara ya karya ba domin rabin abin da ya kamata ya shiga ne domin biyan buƙatar al'ummar Falasɗinawa.

Tashar dai wadda jami'an Amurka suka fara sanarwa a watan Maris ta ƙunshi ɓangarori guda biyu da suka haɗa da gada da aka haɗa da ƙarfe mai hannu biyu mai tsawon mita 548 da kuma ita kanta tashar da ake sauke kayan a kai.

Ita kuma tashar tana kunshe da ƙarafunan da suka haɗu da juna da kuma suka sada ta da ruwan da take kai.

A ranar Talata, jami'an Amurka suka shaida wa kafar watsa labarai ta CBS cewa wani ɓangare na hanyar tashar ta ɓalle sakamakon ruwa mai ƙarfi.

Kamfanin dillanci labarai na Reauters ya rawaito mai magana da yawun Hukumar Abinci ta Duniya, yana cewa Majalisar Dinkin Duniya ta kai tallafi mai yawan manyan motoci 137 daga tashar da ta ruguje - wato kwatankwacin tan 900 tun bayan da aka fara amfani da tashar.

Duk da irin yanayin da ake ciki na buƙatar tallafi a Gazar, firaiministan Isra'ila, benjamin Netanyahu ya dage cewa zai yi nasara a kan ƙungiyar Hamas a Rafah, wani wuri na ƙarshe da ƙungiyar ke da ƙarfi a kudancin zirin.

Yaƙin da sojojin Isra'ila ke yi a Gaza ya fara ne dai tun bayan da dakarun Hamas suka kai hari Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda mutum kimanin 1,200 suka mutu sannan suka yi garkuwa da mutum 252 zuwa Gaza.

Fiye da Falasɗinawa 36,000 ne aka kashe a yaƙin da Isra'ila ke yi a gazar tun bayan harin na ranar 7 ga watan Oktoban kamar yadda ma'aikatar lafiya da Hamas ke iko ta faɗa.

People are also reading