Home Back

Gwamnatin Tarayya ta Haramta Amfani da Wasu Nau'in Robobi

legit.ng 2024/7/5
  • Gwamnatin tarayya ta fara daukar mataki domin magance gurbata yanayi da dumamarsa da kayayyakin roba ke yi a fadin kasar nan, inda ta ba ma’aikatan umarni kan amfani da robobi
  • Ministan muhalli, Iziaq Adekunle Salako ya shaidawa manema labarai cewa daga yanzu an haramta amfani da kayan robobi da ake amfani da su sau daya kawai a yasar
  • Iziaq Salako ya kara da cewa wannan na nuna jajircewar gwamnatin tarayya na magance dumamar yanayi, gurbata shi da kashe wasu halittu da robobin ke yi a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya ta dauki gabarar magance gurbata yanayi da ake yi da robobi da leda ta hanyar haramta amfani da su sau daya kawai a ma’aikatu da hukumoni.

Masu sharhi kan al’amuran muhalli ke kokawa kan yadda zubar da ledoji barkatai da sauran kayan roba na gurbata muhalli tare da taimakawa wurin jawo dumamar yanayi.

Iziaq Kunle Salako
Gwamnati ta dauki mataki kan gurbata muhalli Hoto : Iziaq Kunle Salako Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Ministan muhalli, Iziaq Adekunle Salako ne bayyana matakin da gwamnati ke shirin dauka ga manema labarai a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamnati za ta tsaftace muhallli" - Adekunle

Gwamnatin tarayya ta bakin ministan muhalli, Iziaq Adekunle Salako ya bayyana cewa za a dauki matakan da za su kare muhalli a Najeriya, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Mista Iziaq Adekunle Salako ya kara da cewa daga yanzu ba a amince da ma’aikatan gwamnati a ma’aikatu da hukumomi su yi amfani da roba da ake amfani da ita sau daya a jefar ba.

Ministan ya kara da cewa ana fuskantar babbar matsala ta gurbata muhalli da kayayyakin roba, kuma gwamnatin na kokarin ganin an samu magance tta sannu a hankali.

Mamakon ruwa ya jawo ambaliya

A wani labarin kun ji mamakon ruwan sama da aka tafka a babban birnin tarayya Abuja ya yi haddasa ambaliyar ruwa a yankin rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe a tarayyar.

An shiga fargaba bayan ruwan ya tafi da mutane biyu da ake kyautata zaton sun riga mu gidan gaskiya, yayin da wadanda abin ya shafa su ka nemi daukin ministan Abuja Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

People are also reading