Kwankwaso Ya Shiga Babbar Matsala, Jam’iyyar APC Ta Nemi Jami’an Tsro Su Kama Shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke Rabiu Kwankwaso, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP.
An ruwaito cewa Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da kyankyasar sababbin ‘yan ta’adda a Kano.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya nemi a kama Kwankwaso a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani bangare na sanarwar da Alhaji Abbas ya fitar na cewa:
“Akwai bukatar jami’an tsaron Najeriya su gaggauta kama Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, su kuma tilasta shi ya bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a jihar.”
An ce tsohon gwamnan na Kano ya yi wannan ikirarin ne a ranar Litinin, wajen bikin kaddamar da aikin gina titin karkara mai tsawon kilomita 85 a mahaifarsa Madobi.
Da yake martani kan wannan zargi, Alhaji Abbas ya roki jami'an tsaro da su tsare Kwankwaso har sai ya fadi sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a jihar, in ji rahoton Vanguard.
Shugaban ya yi nuni da cewa wadannan kalamai na nuni ne da wata muguwar manufa da Kwankwaso da makarrabansa suke da ita na kawo tashin hankali a Kano.
Tun da fari, mun ruwaito cewa Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu na kyankyasar wasu sababbin nau’in ‘yan ta’adda a Kano.
Kwankwaso ya yi zargin ne saboda yadda aka jibge jami’an tsaro a karamar hukumar Nasarawa inda Sarkin Kano na 15,Aminu Ado Bayero ke gudanar da sarautarsa a yanzu.
Asali: Legit.ng