Home Back

Gwamnan jihar Kano ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ƙasa ta Tal’udu

dalafmkano.com 2024/5/19

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a shataletalen Tal’udu, da ke ƙaramar hukumar Gwale, domin samar wa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Gwamnan yanyi wannan jawabin ne da yammacin yau Asabar yayin da yake ƙaddamar da aikin.

Haka kuma gwamnan ya ce gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, hakan ya sa yanzu haka gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin.

Har ila yau, gwamna Abba Kabir, ya ce yanzu haka gwamnatin sa ta shirya tsaf wajen bayar da tallafi ga matasa, domin samar musu da hanyoyin sana’o’in dogaro da kai.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙara da cewa an samo kamfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanin lokaci.

People are also reading