Home Back

“Abu 1 da Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Litar Fetur Ta Karye Zuwa Ƙasa da N300” in Ji MEMAN

legit.ng 2024/6/29
  • Kungiyar manyan dillalan mai ta kasa (MEMAN) sun ƙaryata wannan rahoton cewa za a dawo sayar da litar fetur kasa da N300
  • Kungiyar MEMAN ta yi nuni da cewa gwamnati ta fifita matatun cikin gida wajen samar masu da danyen mai hakan zai tabbata
  • Shi ma tsohon shugaban kungiyar MEMAN, Tunji Oyebanji ya ce ba za a iya sauke farashin fetur kasa da N700/lita a halin yanzu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani bangare na 'yan kasuwar mai sun karyata rahoton cewa za a dawo sayar da litar fetur kasa da N300 saboda fara aikin matatun mai na cikin gida.

Dillalan mai sun yi magana kan farashin fetur a Najeriya
Dillalan mai sun karyata rahoton fetur zai sauka kasa da N300/lita. Hoto: Getty Images Asali: Getty Images

Wasu jaridu sun ruwaito cewa farashin fetur zai sauka zuwa kasa da N300 kan kowacce lita da zarar matatar Dangote da sauran matatu sun fara aiki.

Abin da zai karya farashin fetur

Sai dai, kungiyar manyan dillalan mai ta kasa (MEMAN) sun ƙaryata wannan rahoto, suna mai cewa sauke farashin a lokaci daya ba mai yiwuwa ba ne, in ji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar MEMAN ta yi nuni da cewa litar fetur za ta koma kasa da N300 ne kawai idan gwamnatin tarayya ta fifita matatun cikin gida wajen samar masu da danyen mai.

Kungiyar wadda ta ce matatun kasashen waje sun fi na cikin gida samun danyen man, sun ce:

"Kamfanonin da dama ne a yanzu ke cin moriyar shigo da man fetur, duk da hakan na cutar da Najeriya."

Inda matsalar tsadar fetur ta ke

Sakataren yaɗa labarai na kungiyar mamallakan matatun mai na Najeriya (CORAN), Eche Idoko ya bayyana cewa:

"Idan har muka fara sarrafa man fetur mai yawa, kuma muna samun danyen mai wadatacce, to ba makawa hakan zai karya farashin fetur zuwa kasa da N300 kan kowacce lita.
"Me ya sa 'yan Najeriya za su rika sayen litar fetur kan N700 alhalin muna da matatun da za su taimaka wajen rage farashin? Saboda akwai kamfanonin waje da ke amfana da hakan."

Fetur zai iya sauka kasa da N700/ltr?

A zantawarsa da Channels a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar MEMAN, Tunji Oyebanji ya ce ba za a iya sauke farashin fetur kasa da N700 a halin yanzu ba.

A cewar Tunji Oyebanji:

"Gangar danyen mai na dauke da lita 159. A yanzu ana sayar da ganga a kan $80. Idan ka rubanya hakan da N1,400 zai ba ka N112,000 kan kowacce gangar danyen mai.

"Idan ka raba N112,000 zuwa gida 159, zai ba ka N702 kan kowacce litar danyen mai. A haka babu kudin tace man, kudin jigila, da sauran wahalhalu, ka ga sauke farashi ba zai yiwu ba."

Gwamnatin Delta ta haramta yin acaba

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Delta ta haramta yin acaba a fadin jihar tare da ba 'yan sanda umarnin murkushe duk wani babur da aka kama.

A cewar gwamnatin jihar, haramta acaba a ya zama dole saboda karuwar laifuffukan da ake yi da baburan da kuma yawaitar barnar da ake samu a jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading