Harin Bam: Rundunar Sojojin Najeriya ta Fadi Yadda Za Ta Yi da 'Yan Ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa an samu karuwar wadanda suka rasu a harin da 'yan ta'adda su ka kai Gwoza.
Zuwa yanzu, an tabbatar da rasuwar mutane 20, yayin da wasu 52 su ka samu mugayen raunuka kuma yanzu haka suna karbar magani.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa hedikwatar tsaron kasar nan za ta mayarwa 'yan ta'addan zazzafan martani cikin kankanin lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar sojojin kasar ta bayyana shirin maganin 'yan ta'addan da su ka kai mummunan hari Gwoza a jihar Borno har ya kashe mutane 20.
Hedikwatar tsaron kasar nan (DHQ) ta ce za ta tabbatar da kashe 'yan ta'addan da suka kai harin ba tare da bata lokaci ba.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa daraktan yada labarai na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ya ce 'yan kunar bakin wake uku ne suka tayar da bama-baman.
Ya ce an yi nasarar dakile hari na hudu bayan an gano mai dauke da bam din da wuri, wanda ya hakan ya sa ta kashe kanta ita kadai.
A wani labarin, kun ji cewa sojojin kasar nan sun kashe akalla 'yan bindiga 188 tare da kama wasu 330 da ake zargi da kawo tarnaki a kasar nan.
Daraktan yada labaran hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa wannan alama ce na cewa za a kawo karshen ta'addanci a Najeriya.
Asali: Legit.ng