Home Back

Hajjin 2024: Allah Ya Yiwa Wani Alhaji Daga Najeriya Rasuwa a Makkah

legit.ng 2024/7/2
  • Allah ya yi wa ɗaya daga cikin alhazan Najeriya daga jihar Legas, Idris Oloshogbo rasuwa a Makkah bayan ya dawo daga ɗawafi
  • Babban sakataren hukumar jin daɗin alhazai na jihar, Saheed Onipede ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Laraba
  • Ya ce tuni aka yiwa marigayin janaza bisa dokokin hukumomin Saudiyya suka shinfida, kana ya roƙi Allah ya gafarta masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rahotanni sun nuna cewa ɗaaya daga cikin alhazan jihar Legas mai suna, Idris Oloshogbo, ɗan kimanin shekaru 68 a duniya ya rasu a ƙasa mai tsarki.

Likitocin ƙasar Saudiyya ne suka tabbatar da rasuwar Alhaji Oloshogbo a birnin Makkah.

Maniyyaci daga Legas ya rasu.
Jihar Legas ta rasaɗaya daga cikkn alhazanta a ƙasa mai tsarki Hoto: Inside The Haramain Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Oloshogbo ya rasu ne jim kadan bayan ya dawo daga ɗawafin Ka’aba a Makkah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Legas, Saheed Onipede, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun hukumar, Taofeek Lawal, ranar Laraba.

A cewar Onipede, marigayin wanda ya fito daga karamar hukumar Shomolu a jihar Legas ya rasu ne a lokacin da yake cin abincinsa da yamma bayan Sallar Magriba.

Duk da har yanzu likitoci ba su bayyana asalin abin da ya zama ajalinsa ba, Onipede ya ce lamarin ba zai rasa alaƙa da hawan jini ba da kuma yadda ya jigata.

Ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin mamacin a madadin gwamnatin jihar Legas.

Onipede ya roki Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma ba shi Aljanar Firdausi da ladan aikin Hajji, tunda ya riga ya yi niyya.

Don haka ya yi kira ga sauran alhazai da su yi taka-tsan-tsan tare da kiyaye cikaw kansu tun kafin a fara aikin Hajji na hakika wand ya zama wajibi.

"An yi jana'izar marigayin a Makkah bisa ka'idojin da hukumomin Saudiyya suka shimfida," in ji Onipede.

Wani ma’aikacin hukumar Waheed Shonibare ya jagoranci wasu jami’an gwamnatin jihar da wasu mahajjata wajen gudanar da sallar janaza ga mamacin a masallacin Ka'abah.

An biyawa yaro kuɗin hajji

A wani rahoton kuma An karrama yaron da ya nuna hazaka a kan hadda da sanin ma'anonin Alkur'ani a jihar Kano da kujerar zuwa aikin Hajji.

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ce ta bayyana kyautar tare da bayyana dalilai da suka sa aka karrama mahaddacin.

Asali: Legit.ng

People are also reading