Home Back

NELFund: Gwamnati Ta Rufe Ba da Rancen Kuɗi Ga Ɗaliban Manyan Makarantun Jihohi

legit.ng 6 days ago
  • Hukumar kula da asusun NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin karatu
  • A cewar wata sanarwa da NELFund ta fitar a ranar Talata ta ce dakatarwar za ta ba makarantun damar dora bayanan dalibansu
  • Hukumar ta koka kan yadda ƙalilan daga cikin manyan makarantun suka dora bayanan dalibansu domin tantancewa da neman rancen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da asusun ba ɗalibai rancen kudin karatu NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin.

Hukumar ta sanar da dakatarwar wadda za ta dauki tsawon kwanaki 14 biyo bayan karancin daliban manyan makarantun jihohi da ke neman bashin.

NELFund ta yi magana kan daliban manyan makarantun jihohi
NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantu jihohi rancen kudi. Asali: Facebook

A ranar Talata ne The Punch ta ruwaito hukumar NELFund ta ce dakatarwar ya zama wajibi saboda gazawar manyan makarantun na dora bayanan dalibansu a shafinta na intanet.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NELFund ta dakatar da ba dalibai rance

Hukumar wadda ta fitar da sanarwar a Abuja, ta ce har kawo yanzu kalilan ne daga manyan makarantub jihohin kasar ne suka dora bayanin dalibansu domin tantancewa.

Sanarwar ta ce:

"Mun dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin saboda ƙalilan daga makarantun ne suka dora bayanan dalibansu a shafinmu.
"Jami'o'i 20 cikin 48, kwalejoji 12 cikin 54, kwalejin kimiyya 2 cikin 49 na jihohi ne kawai suka iya dora bayanan dalibansu.
"Gazawar manyan makarantun jihohi na dora bayanan dalibansu zai kawo cikas ga kokarinmu na ganin mun tantance masu neman rancen kudin."

Yaushe NELFund za ta janye dakatarwar?

Sanarwar ta yi bayanin cewa dakatarwar za ta fara aiki daga ranar 25 ga watan Yunin 2024 zuwa ranar 10 ga watan Yulin 2024 in ji rahoton The Guardian.

Hukumar ta ce wannan zai ba manyan makarantun jihohi damar dora bayanan dalibansu a shafin hukumar na intanet domin tantancewa.

Hukumar NELFund ta kara jaddada muhimmancin ba da lamunin ga dalibai wanda ta ce zai taimaka wajen ganin dalibai sun yi karatu mai zurfi.

Abba zai gwangwaje manoma da taki

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince a sayo takin Naira biliyan 5 domin tallafawa manoman jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, Abba ya ce tallafin zai bunkasa noma da kuma tabbatar da wadatuwar abinci a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading