Home Back

Ana Shirin Zaben Gwamna, Jigon PDP Ya yi Maƙarƙashiya, Jam'iyya ta Kore Shi

legit.ng 2024/7/1
  • Jam'iyyun siyasa na kara shiri yayin da zaɓen gwamna ke ƙara kusantowa a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya
  • Jam'iyyar PDP ta sanar da korar jigonta kuma tsohon dan majalisar tarayya, Omoregie Ogbiede-Ihama bisa laifi da ya aikata
  • PDP ta ce ta kori Omoregie Ogbiede-Ihama ne biyo bayan tattaunawa da shugabannin jam'iyyar a mazabar Oredo suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Jam'iyyun siyasa a jihar Edo na kara daura damara domin tunkarar zaben gwamna da za a yi a jihar a watan Satumba mai zuwa.

Jam'iyyar PDP a jihar ta kori tsohon dan majalisar tarayya, Omoregie Ogbiede-Ihama bisa zargin saɓa dokokin jam'iyya.

Omoregie Ogbiede-Ihama
PDP ta kori Omoregie Ogbiede-Ihama a jihar Edo. Hoto: Hon. Omoregie Ogbiede-Ihama Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban PDP na yankin Oredo, Lawrence Aguebor ne ya sanar da korar tsohon dan majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da Omoregie daga PDP

Shugaban jam'iyyar PDP a yankin Oredo, Lawrence Aguebor ya ce ba wannan ne matakin farko da jam'iyyar ta dauka a kan Omoregie Ogbiede-Ihama ba.

Lawrence Aguebor ya ce tun a watan Maris jam'iyyar ta dauki matakin dakatar da tsohon dan majalisar na tsawon kwana 30.

Shugaban ya ce kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar ya nemi Omoregie domin ya gurfana a gabansa amma ya ki amsa gayyatar kwamitin.

Jam'iyyar PDP ta kori Omoregie

Lawrence Aguebor ya ce biyo bayan kin amsa kiran kwamitin ne jam'iyyar ta zauna domin duba lamarinsa, a cewar rahoton Channels Television.

A karshe, Lawrence Aguebor ya ce jam'iyyar ta yanke shawarin korar Omoregie Ogbiede-Ihama daga PDP saboda rashin ladabi da ya nuna.

Shugaban jam'iyyar ya ce tun a karon farko an zargi Omoregie Ogbiede-Ihama ne da aikata laifin juyawa jam'iyyar PDP baya a jihar.

APC ta yi alwashi kan zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Edo, Abdullahi Ganduje ya sha alwashi kan samun nasara a zaben.

Shugaban jam’iyyar ya ce APC ta na da tabbacin samun nasara saboda dan takarar da ta tsayar mai kyau ne kuma zabin al’ummar jihar ne.

Asali: Legit.ng

People are also reading