Home Back

Gwamnan Kano Ya Yi Abin a Yaba, Ya Je Ta’aziyyar Kwamandan Ƴan Banga da Aka Kashe

legit.ng 4 days ago
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gudanar da ziyarar ta'aziyya ga iyalan kwamandan 'yan banga da aka kashe
  • Gwamna Abba Yusuf ya kuma kai ziyarar ta'aziyya ga wasu iyalai guda biyu a wurare daban daban na cikin kwaryar Kano a makon nan
  • Mai girma gwamnan ya yi addu'ar Allah ya jikan mamatan tare da yi masu rahama kamar yadda ya fitar da sanarwa a ranar Talata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake yin wani abin azo a gani yayin da ya taka da kansa har gidan wani kwamandan 'yan banga da 'yan ta'adda suka kashe.

Mai girman Abba Yusuf ya ziyarci iyalan dan bangar a rukunin gidajen Soron Dinki da ke Kano City domin yin ta'aziyyar mamacin.

Gwamnan Kano ya kai ziyarar ta'aziyya gidan kwamandan 'yan banga da aka kashe
Gwamna Abba ya je ta'aziyya gidan kwamandan 'yan banga da aka kashe a Kano. Hoto: @Kyusufabba Asali: Twitter

Gwamnan da kansa ne ya wallafa batun ziyarar tare da dora hotuna a shafinsa na X a daren ranar Talata, 2 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya je ta'aziyyar kwamandan 'yan banga

A cewar Abba Yusuf:

"A jiya ne na je unguwar Soron Dinki da ke cikin birnin Kano domin jajantawa iyalan wani kwamandan ‘yan banga da wasu ‘yan ta’adda suka kashe kwanan nan.
Mun wuce zuwa rukunin gidajen Alfindiki, domin sake yin wata ziyarar ta'aziyya ga iyalan Hajiya Aishatu Nasidi."

Gwamna ya yi addu'a ga mamatan

Gwamna Abba ya kuma ce sun karkare ziyarar ta'ziyyar ne da gidan Injiniya Khalil da ke rukunin gidajen Sharada, duk a cikin kwaryar Kano.

Ya yi addu'ar Allah ya jikan mamatan tare da yin rahama a gare su.

Ziyarar gwamnan na zuwa ne jim kadan bayan ganawarsa da masu aikin kwangilar gina tituna a kananan hukumomi 44 na jihar a gidan gwamnatin Kano.

Kalli hotunan ziyarar da gwamnan ya wallafa a kasa:

Matar mataimakin gwamna ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya yiwa uwar gidan mataimakin gwamnan jihar Neja, Hajiya Zainab Garba Tukur rasuwa a ranar Talata.

Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya yiwa marigayiyar addu'a da kuma ba mataimakin nasa hakurin jure wannan rashi.

Asali: Legit.ng

People are also reading