Gwamnan Kano Ya Yi Abin a Yaba, Ya Je Ta’aziyyar Kwamandan Ƴan Banga da Aka Kashe
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake yin wani abin azo a gani yayin da ya taka da kansa har gidan wani kwamandan 'yan banga da 'yan ta'adda suka kashe.
Mai girman Abba Yusuf ya ziyarci iyalan dan bangar a rukunin gidajen Soron Dinki da ke Kano City domin yin ta'aziyyar mamacin.
Gwamnan da kansa ne ya wallafa batun ziyarar tare da dora hotuna a shafinsa na X a daren ranar Talata, 2 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Abba Yusuf:
"A jiya ne na je unguwar Soron Dinki da ke cikin birnin Kano domin jajantawa iyalan wani kwamandan ‘yan banga da wasu ‘yan ta’adda suka kashe kwanan nan.
Mun wuce zuwa rukunin gidajen Alfindiki, domin sake yin wata ziyarar ta'aziyya ga iyalan Hajiya Aishatu Nasidi."
Gwamna Abba ya kuma ce sun karkare ziyarar ta'ziyyar ne da gidan Injiniya Khalil da ke rukunin gidajen Sharada, duk a cikin kwaryar Kano.
Ya yi addu'ar Allah ya jikan mamatan tare da yin rahama a gare su.
Ziyarar gwamnan na zuwa ne jim kadan bayan ganawarsa da masu aikin kwangilar gina tituna a kananan hukumomi 44 na jihar a gidan gwamnatin Kano.
Kalli hotunan ziyarar da gwamnan ya wallafa a kasa:
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya yiwa uwar gidan mataimakin gwamnan jihar Neja, Hajiya Zainab Garba Tukur rasuwa a ranar Talata.
Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya yiwa marigayiyar addu'a da kuma ba mataimakin nasa hakurin jure wannan rashi.
Asali: Legit.ng