Home Back

An Fitar Da Alkaluman Awon Yadda Ake Hade Ayyukan Masana’antu Da Fasahar AI A Sin

leadership.ng 2 days ago
An Fitar Da Alkaluman Awon Yadda Ake Hade Ayyukan Masana’antu Da Fasahar AI A Sin

A yau Alhamis 4 ga watan nan ne aka bude taron masu ruwa da tsaki na kasa da kasa na shekarar 2024, game da kirkirarriyar basira ko AI, da taron manyan jami’ai game da jagorancin AI a duniya, a cibiyar nune-nunen fasahohi dake birnin Shanghai na kasar Sin.

Yayin zaman dandalin karfafa sabon salon zamanantar da masana’antu ta amfani da fasahar AI, an fitar da alkaluman awon yadda ake hade ayyukan masana’antu da fasahar AI a kasar Sin na shekarar nan ta 2024.

A wannan gaba da ake samun gagarumin ci gaba a fannin aiwatar da fasahohin AI, ana ta fadada aiwatar da tsare tsaren cin gajiyar fasahar AI a masana’antu. Inda alkaluman awon yadda ake hade ayyukan masana’antu da fasahar AI a kasar Sin ke mayar da hankali ga cimma tafarkin bunkasar da fasahar AI ke samu a gida da ketare, da bin diddigin ci gaba, da ingancin hade fasahohin AI da bunkasar masana’antu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

People are also reading