Home Back

'Yan Daba Sun Yi Yunƙurin Kai Farmaki Fadar Gwamnatin Kano Yayin Rantsar da Ɗan Kwankwaso

legit.ng 2024/5/2
  • Wasu ƴan daba sun yi yunkurin kawo hargitsi a bikin rantsar da sabbin kwamishinoni a fadar gwamnatin jihar Kano
  • SP Haruna Kiyawa ya bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar cafke su ba tare da sun cimma burinsu ba
  • Kwamishinan ƴan sandan Kano ya ce duk wani zagayen ƴan jagaliya muhimman wurare ya zo ƙarshe, rundunar za ta ɗauki matakai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane 8 da ake zargi da yunkurin kawo cikas a bikin rantsar da sabbin kwamishinoni hudu a gidan gwamnatin Kano.

Lamarin dai ya faru ne a yayin bikin rantsarwar wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a ɗakin taron majalisar zartaswa na fadar gwamnati.

CP Gumel na jihar Kano.
An damƙe wasu ƴan daba 8 da suka yo yunkurin tada yamutsi a fadar gwamnatin Kano Hoto: Kano Police Command Asali: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da kama waɗanda ake zargin ranar Alhamis, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, wadanda ake zargin sun yi haifar da barazana ga tsaro a gidan gwamnati, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka dauki matakin gaggawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Usaini Gumel, ya gargadi duk wasu ‘yan daba bata-gari da masu daukar nauyinsu da su nisanci harkokin gwamnati.

CP ya jaddada cewa duk jami'an tsaro ba za su yi ƙasa a guiwa wajen ɗaukar matakin daƙile duk wani yunƙuri na tada tarzoma da kawo cikas ga tsaro.

"Batun ƴan jagaliya da ke zagayawa a gidan gwamnati, sakatariyar Audu Bako da sauran ofisoshi ya zo ƙarshe," in ji Gumel.

Ya kuma bayyana cewa shugaban ƴan daba 8 da aka kama, wanda ya nuna bai saduda ba, shi ne ya jagoranci yaransa zuwa ɗakin taron da ake rantsarwar.

A cewarsa, yunkurin da yan daban suka yi ya ja hankalin yan sanda da ke sintiri a wurin, wanda nan take suka cafke su kuma suka ci gaba da sa ido.

An kuma gano cewa ƴan daban da aka kama magoya bayan wani ɗan siyasa ne da ke yunƙurin karya doka da oda.

Yan sanda sun karbe sakateriyar APC

A wani rahoton kun ji cewa Jami'an rundunar ƴan sanda sun ƙara kwace iko da sakatariyar tsagin APC wanda Kwamared Austin Agede ke jagoranta a jihar Benue.

Rahoto ya nuna cewa tun da farar safiya ƴan sanda suka girke motocin su, suka toshe duk wata hanya ta shiga sakateriyar a Makurɗi.

Asali: Legit.ng

People are also reading