Home Back

Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 2 A Gidan Yari Kan Satar Doya

leadership.ng 2024/6/1
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

Wata Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya, Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin satar doya da darajarta ya kai Naira 144,000.

An yanke masa hukuncin ne kan laifin aikata laifuka da sata, amma ya roki kotun da ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun Jacinta Okeke, ta yanke wa Sani hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu ko kuma yin aiki a kasuwar Gwagwalada.

Ta kuma gargade shi da ya guji aikata laifuka.

Tun da farko, lauya mai shigar da kara, Abdullahi Tanko, ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara, Liasu Saidu, na kauyen Ukara, ya kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda a ranar 9 ga watan Mayu.

Tanko, ya ce wanda aka yankewa laifin ya kutsa kai cikin gonar wanda ya kai karar ya tuge masa doyar da ya shuka wadda kudinta ya kai Naira 144,000.

A cewarsa laifin ya sabawa sashe na 348 da na 287 na kundin laifuffuka.

People are also reading