Home Back

Mali da Nijar da Burkina sun juya wa ECOWAS baya

dw.com 2024/10/5
Shugaba  Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina Faso
Shugaba Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina Faso

Shugabannin uku bayan da suka jajanta wa al'ummar kasashensu kan mace-macen da ayyukan ta'addanci ke haddasawa, sun nuna jajircewarsu tare da cigaba da yakar kungiyoyin masu da'awar jihadi a yankin Sahel.

A karon farko, kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da suka kwace mulki da tsinin bindiga daga hannun farar hula sun yi taron koli a karkashin kungiyar kawance ta AES.

Shugabannin sun kafa kungiyar kawancen yankin Sahel wato AES  bayan fice wa daga ECOWAS  sakamakon dakatar da su daga harkokin kungiyar. Dama dai kasashen sun yanke alaka da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, inda suka karkata alakarsu da kasar Rasha.

Mahalarta taron kolin na Nijar sun rattaba hannu kan yarjejenioyin bunkasa tattalin arziki da shige da fice da tsaro da inganta hulda a tsakaninsu ta fannoni da dama.

Karin bayani : Nijar: Amurka za ta kammala janye sojojinta

Shugabannin kasashen uku sun zabi shugaban kasar Mali a matsayin shugaban gamayyar kungiyar ta AES a tsawon shekara daya, sannan kasar Burkina Faso za ta karbi bakuncin taro na gaba da shugabannin za su halarta, a gefe guda, shugabannin kungiyar ECOWAS za su gudanar da taron koli a Najeriya a ranar Lahadi.

People are also reading