Bayan Gama Bincike, Tsohon Gwamnan CBN Ya Gamu da Sabuwar Matsala Babba a Mulkin Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta shigar da sababbin tuhume-tuhume 26 kan tsohon gwamnan babban banki CBN.
Sababbin tuhume-tuhume da EFCC ta shigar kan Godwin Emefiele sun ƙunshi zargin hannu a cin hanci da almundahana a lokacin da ya jagoranci CBN.
Kamar yadda Channels tv ta tattaro, za a sake gurfanar da Emefiele a gaban babbar kotun jihar Legas da ke zama a Ikeja ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a sake gurfanar da tsohon gwamnan CBN a gaban kotu bisa laifukan da suka hada da karban na goro, albarkar ofis ta hannun wakilai, da cin hanci da rashawa.
Haka kuma ana tuhumar Emefiele da mallakar kadarori ta hanyar zamba, da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan huldarsa wanda ya saɓa dokar cin hanci ta 2000.
A ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu ne mai gabatar da kara na hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN) ya shigar da kwafin takardar sababbun tuhume-tuhumen a kotu.
A rahoton Premium Times, tuhumar farko ta ƙunshi:
"...cewa a tsakanin 2022 zuwa 2023 a jihar Legas, kai Godwin Ifeanyi Emefiele ka ba da umarnin fitar da $2,136,391,737.33 ba tare da bin ƙa'ida ba."
A wani rahoton kuma kun ji cewa kwamitin binciken da aka naɗa ya kammala bincike na musamman kan ayyukan CBN karkashin tsohon gwamna, Godwin Emefiele.
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya godewa Mista Jim Obazee da ƴan tawagarsa bisa namijin kokarin da suka yi wajen gudanar da wannan aiki mai rikitarwa
Asali: Legit.ng