Home Back

'Yan Shi'a Za Su Dauki Fansar Rayukan 'Yan Uwansu da Aka Hallaka? El-Zakzaky Ya Magantu

legit.ng 2024/5/19
  • Kungiyar Shi'a a Najeriya ta ƙaryata jira cewa ta na shirin daukar mataki kan kisan 'yan uwansu da aka yi a Kaduna
  • Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky shi ya tabbatar da haka inda ya ce babu kamshin gaskiya a labarin
  • Wannan na zuwa ne bayan kisan matasa bakwai 'yan kungiyar da aka yi a jihar Kaduna kwanaki takwas da suka wuce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kungiyar IMN a Najeriya da aka fi sani da Shi'a ta ƙaryata cewa za ta dauki mataki kan kisan 'yan ƙungiyar.

Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce babu wani shiri na dakar fansa kan abin da ya faru.

El-Zakzaky ya yi martani kan jita-jitar daukar fansa a Kaduna
Shugaban Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya musanta cewa za su dauki fansa kan kisan 'yan uwansu a Kaduna. Hoto: @am_ghoulam. Asali: Twitter

El-Zakzaky ya karyata jita-jitar daukar fansa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Isah Hassan Mshelgaro ya fitar a madadin kungiyar ta kasa, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mshelgaro ya ce rundunar 'yan sanda ta yada wani sako da ke nuna cewa 'yan Shi'a na shirin daukar mataki bayan kisan 'yan uwansu da aka yi a Kaduna.

Kungiyar ta ce ana yada sakon ga sauran ofisoshin rundunar 'yan sanda domin a yada shi ya zagaya ko ina.

El-Zakzaky ya kadu da labarin daukar fansar

Ta ce Sheikh Zakzaky ya kadu da samun sakon da 'yan sandan ke yadawa kan shirin daukar matakin.

"Muna son sanar da al'umma cewa babu wani shiri na daukar fansa kan kisan 'yan uwanmu guda bakwai da aka yi a jihar Kaduna kan 'yan sanda ko wata kungiyar ko jama'a."
"Wannan abin kunya ya fito ne daga hedkwatar 'yan sanda daga jihar Borno wacce nisanta da jihar Kaduna ya kai kilomita 800."

- Cewar kungiyar

Kungiyar ta kara da cewa a shekarun bayan an hallaka mambobinta da dama amma ba ta dauki mataki ba, sai dai kuma hakan bai kuma ba ya na nufin ba su san me suke ba.

Ta ce duk abubuwan da suka faru akwai ranar da adalci zai bayyana amma dai ba za su taba mantawa ko yafewa ba, cewar Peoples Daily.

An kara da 'yan sanda da Shi'a

Kun ji cewa cewa rigima ta barke a jihar Kaduna yayin da aka kaure tsakanin 'yan Shi'a da rundunar 'yan sanda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla 'yan kungiyar bakwai aka hallaka yayin rikicin a Zaria da cikin Kaduna.

Asali: Legit.ng

People are also reading