Home Back

Rikicin Masarautar Kano: Babu Hawan Sallah a Kano bana – Rundunar Ƴan sandan Kano

premiumtimesng.com 2024/9/21
Rikicin Masarautar Kano: Babu Hawan Sallah a Kano bana – Rundunar Ƴan sandan Kano

Rundunar Ƴan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi a jihar Kano a bana.

Kakakin rundunar Ƴan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.

”Haka kuma an haramta duka nau’ukan hawan sallah a lokacin bukukuwan babbar sallah”

Ƴan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.

Daga nan sai suka shawaraci mazauna jihar da su gudanar da sallar idinsu cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka saba, ba tare da tashin hankali ba.

“Don haka muna kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusanci.

A ranar 23 ga watan Mayun 2024 gwamnan Abba Yusuf ya sanar da naɗa Muhammadu Sanusi II, a matsayin sarkin Kano na 16, bayan sauke Aminu Ado Bayero da kuma rushe ƙarin masarautun da gwamnatin Ganduje ta yi a shekarar 2019.

Sai dai kuma tun bayan sanar da haka aka raba jiha tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu.

Yayin da Sarki Sanusi ke riƙe babbar fadar, Aminu Ado ya koma fadar Nassarawa ne can shima yana sarautar sa.

People are also reading