Home Back

Kalubalen Da Ke Gaban Finidi George

leadership.ng 2024/5/18
Finidi

Bayan da hukumar kallon kafar Nijeriya, NFF ta nada Finidi George a matakin sabon kociyan Super Eagles, tuni masana suka fara sharhi a kan irin kalubalen da ke gaban tsohon dan wasan na Nijeriya.

Kafin a nada shi a matsayin koci na dindindin Finidi George ya yi watanni 20 yana aikin mataimakin Jose Santos Peseiro, wanda ya ajiye aikin, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka da Super Eagles ta yi ta biyu a Ivory Coast a bana.

Haka kuma ya ja ragamar tawagar Nijeriya a matakin kociyan rikon kwarya a wasan sa-da zumunta biyu da ta buga a Morocco a watan jiya sannan ya kuma doke Ghana 2-1 a wasan farko, hakan ya kawo karshen rashin nasara a kan Ghana daga Super Eagles cikin shekara 18, amma an doke shi 2-0 a karawa da Mali a wasan na sada zumunta.

George, wanda yana cikin ‘yan wasan da suka dauki kofin nahiyar Afirka a Super Eagles a 1994 a Tunisia, ya buga mata wasanni 62, ya wakilce ta a gasar kofin duniya a 1994 da 1998.

Haka kuma ya lashe lambar zinare da ta azurfa da ta tagulla a gasar kofin nahiyar Afirka a 1992 da 1994 da 2000 da kuma 2002, sannan Finidi mai shekara 52 tsohon dan kwal-lon Ajad da Real Betis ya fara buga wasa a Calabar Robers da Sharks FC daga nan ya je nahiyar Turai ya buga wasa a kungiyoyin Ajad da Real Betis.

Shi ne ya bai wa Rashidi Yakini, kwallon da Nijeriya ta fara ci a gasar kofin duniya a karawa da Bulgaria a Amurka ranar 19 ga watan Yunin 1994, sannan aikin da aka bai wa George shi ne ya yi kokarin ganin ya kai Super Eagles gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Kenan ya zama wajibi Nijeriya ta doke Afirka ta Kudu a Uyo da kuma Jamhuriyar Benin a Abidjan a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da suke gabanta saboda kawo yanzu Super Eagles tana ta uku a rukuni na uku a neman gurbin shiga gasar kofin duni-ya, biye da Rwanda da kuma Afirka ta Kudu.

Banda gasar cin kofin duniya da ake fatan Finidi zai iya jagorantar Nijeriya, akwai buka-tar hada kan ‘yan wasan kasar domin gina sabuwar tawagar da za ta dade ana damawa da ita a fagen kwallon kafa.

Sannan akwai nada sabon kyaftin, bayan da ake ganin abu ne mai wahala dan wasa Ahamd Musa ya ci gaba da zama kyaftin din tawagar ta Super Eagles, nan ma wasu suna ganin dan wasan baya kuma mataimakin Ahmad din, William Trost-Ekong, wanda kusan shi ne ya jagoranci tawagar har aka kammala wasannin Afirka da Nijeriya ta je wasan karshe shi ne ya kamata ya zama jagoran Super Eagles din.

Wani abu da ake fatan Finidi zai yi shi ne bawa matasa dama domin suma su samu damar bayyana kansu a matsayin ‘yan wasan Super Eagles domin Nijeriya akwai matasan ‘yan wasa da kawai dama suke bukata domin nuna kansu a duniya.

People are also reading