Home Back

An Shiga Jimami Bayan Sojojin Najeriya Sun Hallaka Dan Sanda

legit.ng 2024/7/3
  • Wani sifeton ƴan sanda da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya rasa ransa a yayin faɗa da wasu jami’an sojojin ruwa a unguwar Okokomaiko da ke Legas
  • Ɗan sandan ya kasance yana sintiri ne tare da abokan aikinsa guda huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce sifeton ya yanke jiki ya faɗi kuma an tabbatar da mutuwarsa a asibiti

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Okokomaiko, jihar Legas - Wasu da ake zargin jami’an sojin ruwa ne sun kashe wani sifeton ƴan sanda, wanda ke sintiri tare da wasu abokan aikinsa huɗu a yankin Okokomaiko da ke ƙaramar hukumar Ojo a jihar Legas.

Mummunan lamarin ya faru ne bayan da ƴan sandan suka kama wani ɗan Achaba tare da fasinjansa a kan hanyar Igbo-Elerin bisa laifin karya dokar tuƙi.

Sojoji sun hallaka dan sanda a Legas
Sojojin Najeriya sun hallaka dan sanda a Legas Hoto: @PoliceNG Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust, ta ce wani shaidan ganau ba jiyau ba Shola Shodiya ya ce ɗan Achaɓan da fasinjansa wanda ya yi iƙirarin shi sojan ruwa ne ya ƙi yarda a kama shi inda suka yi ta gardama mai zafi da ƴan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya ce ƴan sandan sun yi ƙoƙarin ƙwace babur ɗin a kusa da gidan mai na Beno da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Hundeyin ya ce mutanen biyu da ke cikin kayan gida sun yi taƙaddama da ƴan sandan tare da wasu jami'ai da suka zo wajen domin marawa abokin aikinsu baya.

"Sauran jami'an sojojin ruwan sanye da Khaki sun iso wajen tare da taimakawa abokin aikinsu. Yayin da sifeto ɗaya ya faɗi a sume, sai sojojin ruwan suka arce daga wajen."
"An ɗauko sifeton sannan aka garzaya da shi zuwa wani asibiti a yankin inda aka tabbbatar da mutuwarsa. An ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawa na Idi-Araba domin binciken gawa. Ana ci gaba da gudanar da bincike."

- Benjamin Hundeyin

Soja ya salwantar da ransa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani sojan Najeriya da ke aiki a jihar Abia ya aikata aika-aikar raba kansa da duniya.

Sojan wanda yake aiki da bataliya ta 144 Forward Operation Base (FOB) da ke High School Ngwa, Abayi, a ƙaramar hukumar Osisioma, ya salwantar da ransa.

Asali: Legit.ng

People are also reading