Home Back

NNPC Zai Karya Farashin Litar Fetur Zuwa N488 a Gidajen Man Najeriya? Gaskiya Ta Fito

legit.ng 3 days ago
  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya musanta ikirarin cewa ya yi sauye-sauye ga farashin man fetur a sassan kasar nan
  • Hakan ya biyo bayan wani rahoto da aka samu cewa NNPC ya amince da sabon farashin fetur zuwa N488 a kan kowace lita
  • Rahoton na karyar ya kuma bayyana cewa farashi mafi tsada da za a sayar da fetur din shi ne N557 kan kowace lita a Arewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya cewa ya zabtare farashin fetur.

Babban jami'in yada labarai na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye ya bayyana cewa rahoton sabon farashin fetur "ƙanzon kurege ne."

NNPC yayi magana akan rage farashin man fetur
NNPC yayi magana akan daidaita farashin man fetur zuwa N488/lita. Hoto: @nnpclimited Asali: Facebook

A zantawarsa da jaridar New Telegraph ta wayar tarho, Mista Soneye ya ce kamfanin NNPC zai fitar da sanarwa ne a hukumance idan ma an samu sauyin farashin fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Soneye ya ce:

"Rahoton sabon farashin ƙanzon kurege ne. A hukumance za mu fitar da sanarwa idan har aka samu sauyin farashin mai."

NNPC ya sauke farashin litar fetur

A cewar wani rahoton "ƙarya" da ya mamaye intanet, NNPC ya umarci dukkanin 'yan kasuwar man Najeriya da su koma sayar da litar fetur kan N488 zuwa N557.

Rahoton ya kara da cewa:

"Umarnin ya fito daga NNPC a ranar Laraba, kuma an aika takardar umarnin ga manya, matsakaita da kananun 'yan kasuwar mai na kasar nan.
"Takardar umarnin ta nuna cewa za a rika sayar da litar fetur kan N557 a Maiduguri da Damataru, sai kuma N550 a sauran jihohin Arewa.
"A kudancin kasar, za a rika sayar da litar man kan N520, N511, N500, amma ban da Uyo inda za a rika sayar da shi kan N515. Legas kuwa zai koma N488."

NNPC ya dauki mataki kan wahalar fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin NNPC ya ce ya dauki matakai da za su taimaka wajen kama masu boye mai wanda hakan ke jawo wahala da tsadar man.

A yayin da NNPC ya ce ya hada kai da jami'an tsaro domin aiwatar da hakan, ya kuma ba ta tabbacin cewa ya tanadi mai da zai ishi Najeriya da dogon lokaci.

Asali: Legit.ng

People are also reading