EFCC: An Bukaci Binciken Abokin Takarar Atiku Abubakar a 2023, Ifeanyi Okowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Kungiya mai yaki da cin hanci da rashawa (NACAT) ta bukaci binciken tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta yi kiran ne ga hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
Shugaban kungiyar, Tega Oghenedoro ya ce abin takaici ne matuka yadda hukumar EFCC ta yi shiru kan tsohon gwamnan duk da cewa an shigar mata da korafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar ya ce mutane da dama da kungiyoyi sun shigar da korafi kan badakalar da ake zargin tsohon gwamnan amma har yanzu hukumar ta kasa tabuka komai. Ga abin da yace:
"Mun rubuta korafi watanni da suka wuce, haka zalika wasu dattawa daga jihar Delta sun shigar da korafi a kan Okowa amma har yanzu babu wani bayani daga EFCC ko ICPC."
-Shugaban kungiyar NACAT, Tega Oghenedoro
Shugaban NACAT ya yi kira ga EFCC kan cewa ya kamata ta fara binciken Ifeanyi Okowa kamar yadda ta fara binciken tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
A cewarsa EFCC tana kyale tsofaffin gwamnoni da suka aikata laifuffukan cin hanci da rashawa daga Arewa amma suna kyale na kudu, rahoton Peoples Gazette.
Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya kasance abokin takarar Atiku Abubakar a karkashin jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar shekarar 2023.
NACAT ta ce idan har hukumar EFCC ba za ta yi halin maza kan kama Ifeanyi Okowa ba to ya kamata ta kyale Yahaya Bello ma kawai.
A wani rahoton, kun ji cewa da alamu hankalin APC ya fara karkata kan yadda dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ke tattaunawa da takwaransa na LP, Peter Obi.
Ana ganin shugabannin biyu na saka labule domin tattaro dabarun kwace mulkin kasar nan daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu a kakar zaben 2027.
Asali: Legit.ng