Home Back

Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 140, Sun Kwato Makamai Masu Yawa

legit.ng 2024/6/30
  • Rundunar sojojin haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) ta bayyana irin nasarorin da ta samu kan ƴan ta'adda a yankin tafkin Chadi
  • Kwamandan rundunar MNJTF ya bayyana cewa sojoji sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 140 a yayin fafatawa da su
  • Sun kuma lalata sansanonin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai masu tarin yawa a hare-haren da aka musu a maɓoyarsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar sojojin haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) da ke aiki a 'Operation Lake Sanity 2' ta ce ta kashe ƴan ta’adda 140.

Rundunar ta kuma bayyana cewa sojoji shida sun rasa rayukansu yayin faɗa da ƴan ta'addan a yankin tafkin Chadi.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a yankin tafkin Chadi
'Yan ta'adda 176 sun mika wuya a yankin tafkin Chadi Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Facebook

Kwamandan rundunar MNJTF, Manjo Janar Ibrahim Sallau, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Maiduguri a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta'adda sun miƙa wuya

Ya bayyana cewa ƴan ta’adda 176 ne suka miƙa wuya bayan an kai hare-hare ta sama yayin da aka cafke wasu mutum 57 bisa zargin aikata ayyukan ta'addanci, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Manjo Janar Ibrahim Sallau ya ce, a cikin watan da ya gabata, dakarun MNJTF sun jajirce wajen aikinsu, inda a baya-bayan nan suka yi nasarar kakkaɓe mafakar ƴan ta'adda a yankin tafkin Chadi.

Ya ce wuraren da sojojin suka fatattaki ƴan ta'adda sun haɗa da Doron Naira, Zanari, Bagadaza, da sauran muhimman wuraren da ƴan ta’adda ke ɓoyewa.

Sojoji sun yi nasara kan ƴan ta'adda

Ya ƙara da cewa, a lokacin da suke gudanar da wannan aiki, sun ƙwato makamai da suka haɗa da harsasai 796, bindigar PKM guda ɗaya, bindigar AK-47 guda biyar, babura biyu, jigida takwas da sauran makamai.

A cewarsa, farmakin ya kuma yi sanadiyyar lalata wasu muhimman sansanonin ƴan ta’adda a Tumbum Fulani, Bagadaza, Zannari, Doron Naira, da sauran muhimman wurare a yankin tafkin Chadi.

Ya ƙara da cewa ƴan ta’addan da suka miƙa wuya tare da waɗanda aka kama a halin yanzu suna tsare inda ake ci gaba da yi musu tambayoyi.

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya da ke aiki da rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda shida a jihar Kaduna.

Sojojin sun kuma cafke wasu mutum uku da ake zargi da haɗa baki da ƴan ta'addan a wani samame na musamman a ƙaramar hukumar Giwa.

Asali: Legit.ng

People are also reading