Home Back

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 9 Da Sace 50 A Jihar Katsina

leadership.ng 5 days ago
AFCON 2023: Ekong Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Duk Da Rashin Nasarar Nijeriya A Wasan Karshe

Akalla mutane tara sun rasa rayukansu tare da kona gidaje da motoci tara, inda aka yi garkuwa da mutane hamsin a wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai kauyen Maidabino da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Harin wanda ya faru a daren ranar Asabar da misalin karfe 7 na dare har zuwa karfe 2:30 na safe ya yi sanadiyar kona wani kantin magani da shaguna sama da 15 a kauyen kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ɗanmusa a majalisar dokokin jihar Katsina, Aminu Sai Baba, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ce an aike da kira ga gwamnati bayan harin da ta dauki matakin gaggawa.

Baba ya ƙara da cewa gwamnati ta amsa kiran na su yayin da aka tura jami’an tsaro yankin domin dawo da zaman lafiya.

Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike tare da bayar da tabbacin samun karin bayani.

Harin dai shi ne na baya-bayan nan a yankin Ɗanmusa da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga ba kakkautawa, wanda ya zo a daidai lokacin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai gudanar da taron tsaro da gwamnonin yankin Arewa maso Yamma da kuma hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) a Katsina, domin magance matsalolin tsaro a yankin.

People are also reading