Home Back

Bayan An Koka da Nade-Nadensa, Tinubu Ya ba Amininsa Mukami a Gwamnatin Tarayya

legit.ng 2024/6/26
  • Bola Ahmed Tinubu ya saurari koke-koken al’umma, ya nada ‘yan kwamitin gudanarwa a manyan makarantun gwamnati
  • Shugaban kasar ya ba Bisi Akande wanda amininsa ne mukami a gwamnatin tarayya da ya tashi rabon kujeru wannan karo
  • Wole Olanipekun wanda ya tsayawa Tinubu da ake gwabzawa a shari’ar zaben shugaban kasa ya samu matsayi a UNILAG

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu nade-naden mukamai a sakamakon korafi da ya biyo bayan abin da aka yi a baya.

Mai girma shugaban kasar Najeriya ya canza mutanen da su rike majalisun gudanar da harkokin jami’o’i da manyan makarantu.

Bisi Akande da Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba Bisi Akande matsayi a Gwamnatin Tarayya Hoto: www.bisiakande.com Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The cable ta ce Bisi Akande yana cikin mutane 255 da suka samu mukamai a manyan makarantun gaba da sakandaren gwamnati.

Kamar yadda Nnamdi Mbaeri ya sanar a wani jawabi, Cif Bisi Akande zai jagoranci majalisar gudanar da harkokin jami’ar Ibadan.

Bisi Akande wanda ya yi gwamna a shekarun baya shi ne shugaban farko na APC a tarihi, yana cikin masu kusanci sosai da Bola Tinubu.

Kwanakin baya aka ji shugaba Bola Tinubu ya ba diyar ‘dan siyasar mukami a gwamnati, Temitope Ilori ta zama shugabar NACA.

Shi kuma lauyan shugaban kasar a kotun zabe, Wole Olanipekun ya zama shugaban majalisar gudanar da harkokin jami’ar Legas.

Wole Olanipekun SAN ya kare shugaba Bola Tinubu a lokacin da Atiku da Peter Obi suka kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa.

Sauran manyan APC da suka samu mukami wannan karo sun hada da Adebayo Shittu wanda ya yi minista a mulkin Muhammadu Buhari.

Rahoton Vanguard ya tabbatar da tsohon ministan sadarwan ya samu kujera ne a jami’ar kiwon lafiya ta David Umahi da ke jihar Ebonyi.

Tsohon mai ba APC shawara a kan harkokin shari’a, Muiz Banire ya zama shugaban wannan majalisa ta jami’ar sufuri ta Daura.

https://www.thecable.ng/full-list-bisi-akande-wole-olanipekun-tinubu-appoints-governing-councils-for-tertiary-institutions/

Rahoto ya zo cewa Malam Kasim Balarabe Musa ya jagoranci zanga-zangar lumunar da aka shirya a ranar 12 ga watan Yunin 2024.

Yaron tsohon gwamnan na Kaduna ya ce ba a taba samun abubuwa sun tabarbare kamar yau ba, ya ba Bola Tinubu shawarar murabus.

Asali: Legit.ng

People are also reading