Bayan An Koka da Nade-Nadensa, Tinubu Ya ba Amininsa Mukami a Gwamnatin Tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu nade-naden mukamai a sakamakon korafi da ya biyo bayan abin da aka yi a baya.
Mai girma shugaban kasar Najeriya ya canza mutanen da su rike majalisun gudanar da harkokin jami’o’i da manyan makarantu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The cable ta ce Bisi Akande yana cikin mutane 255 da suka samu mukamai a manyan makarantun gaba da sakandaren gwamnati.
Kamar yadda Nnamdi Mbaeri ya sanar a wani jawabi, Cif Bisi Akande zai jagoranci majalisar gudanar da harkokin jami’ar Ibadan.
Bisi Akande wanda ya yi gwamna a shekarun baya shi ne shugaban farko na APC a tarihi, yana cikin masu kusanci sosai da Bola Tinubu.
Kwanakin baya aka ji shugaba Bola Tinubu ya ba diyar ‘dan siyasar mukami a gwamnati, Temitope Ilori ta zama shugabar NACA.
Shi kuma lauyan shugaban kasar a kotun zabe, Wole Olanipekun ya zama shugaban majalisar gudanar da harkokin jami’ar Legas.
Wole Olanipekun SAN ya kare shugaba Bola Tinubu a lokacin da Atiku da Peter Obi suka kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa.
Sauran manyan APC da suka samu mukami wannan karo sun hada da Adebayo Shittu wanda ya yi minista a mulkin Muhammadu Buhari.
Rahoton Vanguard ya tabbatar da tsohon ministan sadarwan ya samu kujera ne a jami’ar kiwon lafiya ta David Umahi da ke jihar Ebonyi.
Tsohon mai ba APC shawara a kan harkokin shari’a, Muiz Banire ya zama shugaban wannan majalisa ta jami’ar sufuri ta Daura.
https://www.thecable.ng/full-list-bisi-akande-wole-olanipekun-tinubu-appoints-governing-councils-for-tertiary-institutions/
Rahoto ya zo cewa Malam Kasim Balarabe Musa ya jagoranci zanga-zangar lumunar da aka shirya a ranar 12 ga watan Yunin 2024.
Yaron tsohon gwamnan na Kaduna ya ce ba a taba samun abubuwa sun tabarbare kamar yau ba, ya ba Bola Tinubu shawarar murabus.
Asali: Legit.ng